Akalla matasa 70 ne ‘yan ci-rani daga jihohin Kano, Katsina, Zamfara da Kaduna aka kama a garin Ogomosho na jihar Oyo.
Matasan wadanda aka dauko su daga Arewacin kasar nan, an yi lodin su ne zuwa kudu a cikin tirela, duk kuwa da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi.
An dai yi mamakin yadda su ka wuce jihohi da dama kafin a tare motar wadda ke dauke da su a garin na Ogomosho.
Majiya daga jami’an NSCDC, da ba ta so a ambaci sunan ta, ta ce matasan sun kai su 70, kuma ana ci gaba da tsare su.
“Mun damke su ne wajen jijjifin asubahi, kuma har yanzu ba a ba mu umarnin yadda za mu yi da su ba.”
Jihohi da dama a Arewaci da kudancin kasar nan na ci gaba da damke matasa ‘yan ci-rani ‘yan Arewa da ke kokarin komawa kudancin kasar nan domin xi gaba da gudanar da ayyukan neman abinci a can.
Cikin makon nan Gwamna El-Rufai na Jihar Kaduna ya tilasta an killace waau matafiya au hamshin. Ya bada umarnin a tsare su kwanaki 14 yadda za a gane ko su na dauke da cutar Coronavirus ko ba su da ita.
Nan a Arewa kuma gwamnonin jihohi na ta musayar almajirai daga wannan jiha zuwa waccan, kowace jiha na kyamar ci gaba da zaman almajirai a cikin ta.
Matasalar ta kara zame wa Arewa babbar matsala, ganin cewa Saudiyya za ta maido ‘yan Najeriya 11 masu zaman Tikaranci a kasar.
Cikin makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Jihar Abia ta maido lodin matasan da ta kama dankare cikin shanu makare da tirela zuwa Arewa
Rahoton ya bayyana yadda Jihar Abia ta ki barin gungun wasu matasa daga Arewa su shiga jihar, bayan ta kama su boye a tsakiyar shanun da aka yi lodi cikin tirela a ranar Talata.
Wani bidiyo da aka watsa a shafin Facebook na Gwamnatin Jihar Abia, ya nuna yadda jami’ai suka sa matasan yin layi, suka ana lissafa su daya bayan daya.
Yawancin jihohin kasar nan dai sun hana zirga-zirgar motoci dauke da fasinja zuwa jihar, saboda kokakin hana yaduwa da fantaamar cutar Coronavirus.
“Jami’ai na sun shiga cikin tirelar, sai suka ga dandazon mutane a ciki sun boye karkashin shanu. Su ka ce kowa ya fito.” Haka Kwamishinan Tsaron Jihar Abia, Dan Okoli ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Ya ce motar ta taso daga Arewa, ta keta ta Enugu, ta na kokarin shiga Abia ne aka dakatar da ita.
“Ana lekawa cikin mortar sai ga mutum 11 a tsakiyar shanu, an zakulo su, aka ce su sauko kasa.”
Okoli ya ce matasan ba su iya magana da kowane yare sai Hausa. Wannan ya sa an kasa yi musu wasu cikakkaun tambayoyin da za su iya bada gamsassun bayanai.
Okoli ya ce jami’an sa sun bar direban da shanun da ya ke dauke sun wuce.
“Saboda idan mu ka ce ba za a wuce da shanun ba, to ina tabbatar maka idan suka juya kafin su koma gida duk sun mutu.”
Ya ce ya kara samun rahoto daga jami’an na sa cewa cikin dare sun hana wasu gungun matasa wucewa, wadanda suka kama a cikin motar daukar shank, su kimanin 30.
Ya kara da cewa daga baya ne suka samu labarin cewa matasan da ke shiga su na boyewa ne karkashin shanu a cikin motocin tirela. To daga nan ne ya ce wa jami’an sa su rik shiga cikin kowace tirela mai dauke da shanu, domin zakulo duk wani dan ci-rani daga Arewa, ana fito da shi.
Discussion about this post