Akalla mutum 15 ne wasu mahara suka kashe a kauyen Gonar Rogo dake karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mohammmed Jalige da ya Sanar da haka ranar Talata yacw ‘yan sanda sun lashi takobin kamo wadannan mahara domin a hukunta su.
Jalige ya ce a ranar Talata DPO na Kajuru ya sanar da rundunar cewa wasu mahara akan babura dauke da bindigogi sun far wa kauyen Gonar Rogo a karamar hukumar Kajuru.
Ya ce maharan sun harbe mutum 15 sannan wasu mutum biyar sun ji rauni a jikin su.
Jalige ya ce rundunar ‘yan sanda ta hada kai da kungiyar ‘yan banga dake aiki a kauyen domin farautar wadannan mahara sannan kuma an kai wadanda suka ji rauni asibiti.
Ya kuma ce sun saka jami’an tsaro a kauyen domin hana maimaicin hare-hare irin haka nan gaba.
Jackie ya yi kira ga mutane da su hada hannu da Jami’an tsaro domin kawo karshen miyagun aiyukka a jihar.
Shima shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da jajen sa ga al’ummar wannan Kauye na Gonar Rogo sannan ya yi kira ga mazauna wannan garuruwa da su rika hakuri da juna su dai daukar fansa a kan juna. Haka kakakin fadar gwamnati, Garba Shehu ya rubuta a shafinsa ta tiwita ranar Talata.