Gwamnatin Kaduna ta yi kira da kakkausar murya cewa ba za ta daga wa koma waye kafa ba idan ya nemi shigowa jihar daga wata jiha, cewa hakan karya dokar hana tafiye-tafiye ne.
kakakin gwamnatin Jihar Muyiwa Adekeye ya sanar da haka a takarda da ya rabawa manema labarai a Kaduna ranar Litini.
Ya ce an kama mutum 27 ranar Lahadi, sannan wasu 23 ranar Litinin. Kuma suna nan an killace su sai sun yi kwanaki 14 kafin a sake su tukunna.
Ya kara da cewa yanzu fa babu daga kafa da gwamnati za ta yi wa duk matafiyi, da zaran ya iso iyakar Kaduna, ko dai ya koma inda ya fito ko kuma ya wuce kai tsaye inda ake horas da masu bautar kasa, a killace shi na kwanaki 14, a tabbatar bashi da Korona.
” Dokar gwamnatin Najeriya ya hana tafiye-tafiye saboda haka yin shi karya doka ne.
Haka kuma gwamnati na kira ga jami’an gwamnati dake amfani da ofisoshin su wajen yin tafiye-tafiye tare da iyalan su, cewa hakan karya doka ce kuma suma za a fara maida su inda suka fito, ko su bi sahun killacewa.
” Daga yanzu ba sani ba Sabo ko ka tsaya inda kake zuwa a janye dokar tafiye-tafiye ko kuma jami’ai su maida kai inda kafito, ko kuma ka garzaya wurin horas da masu bautar Kasa kayi zaman kwana 14. Wannan shine zamu yi.
Sannan kuma gwamnati ta bada shawarar mutane su ci gaba da zama a inda suke har sai an janye dokar hana walwala.