Daya daga cikin ‘yan Najeriya da aka dawo da su daga Dubai ya rasu bayan yayi fama da cutar Coronavirus.
Kwamishinan Lafiyar jihar Legas Akin Abayomi, ya bayyana cewa wanda ya rasu na fama da wasu cututtukan baya ga Coronavirus.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa adadin yawan mutanen da ke dauke da cutar Covid-19 da aka sallama a jihar sun kai 502 a jihar.
Ma’aikatar ta ce an Sallami mutum 33 da suka warke daga cutar a jihar ranar Litini.
A lissafe dai adadin yawan mutanen da aka sallama a jihar sun kai kwatan mutanen da suka kamu da cutar kuma ke kwance a asibiti a jihar.
Ma’aikatar ta ce mata 9 da maza 24 na daga cikin mutanen da aka sallama daga asibitocin kula da masu fama da cutar coronavirus dake Onikan da Eti-Osa.
Mutum 1,861 ne suka kamu da cutar a jihar.
Daga ciki 1,308 na kwance a asibiti, an sallami 502, 33 sun mutu.
Kwamishinan Jihar Lagos, Akin Abayomi, ya bayyana cewa sama da kashi 40 na wadanda ake samu dauke da cutar a jihar, ba su yarda a gano takamaimen inda suke, tserewa su ke yi, ballantana a kai su a killace su.
Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar Juma’a, Abayomi ya ce wannan ne dalilin da ya sa ake ganin alkaluman wadanda suka kamu da ciwon a Jihar Legas, amma kuma ga yawan gadaje birjik a cibiyoyin killacewa, babu masu cutar da yawa.
Abayomi ya ce a yanzu ba su da lokacin farautar masu cutar a cikin gari. Abin da ke gaban su shi ne, su na gwada duk wanda suka ga ya na dauke da alamu cutar ne kawai.
Discussion about this post