Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon ministan ayyukan harkokin waje Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa.
Gambari mai shekaru 75, ya rike mukamai da dama a kasa Najeriya da waje da majalisar dinkin duniya.
Gambari zai maye gurbin marigayi Abba Kyari da Allah yayi wa rasuwa a dalilin fama da yayi da Coronavirus.
Sarkin Ilori, Ibrahim Sulu-Gambari, ya aika da sakon godiya ta musamman ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari, bisa wannan nadi da yayi wa Ibrahim Gambari sabon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.
A wasikar, Maimartaba Ibrahim Sulu-Gambari, ya ce wannan abu basu aka yi wa ba kawai, an karrama jihar ne gaba daya.
Discussion about this post