Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 195 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Laraba.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Talata, Jihar Legas ta samu karin mutum 82, 30-Kano, 19-Zamfara, 18-Sokoto, 10-Borno, 9-FCT, 8-Oyo, 5-Kebbi, 5-Gombe, 4-Ogun, 3-Katsina, 1-Kaduna, 1-Adamawa.
Yanzu mutum 3145 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 534 sun warke, 103 sun mutu.
Jihar Kano ta samu karin mutum 30 ranar Laraba. Jihar Zamfara da Suma alkaluma ya nuna sun samu karin wadanda suka kamu da dama.
Jiha kamar Bauchi da ke mutum 80 basu samu karin ko da mutum daya ba a ranar laraba.
Idan ba a manta ba gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya garagadi mutane cewa bai ce a rika shan magungunan da ya rika sha lokacin da yake fama da da cutar Coronavirus ba tare da izinin likita ba. Wato maganin Chloroquine da Zithromax.
Yayi wannan gargadi ne ranar Laraba.
Gwamna Bala ya ce zai janye cewa da yayi wai Chloroquine da Zithromax, da Vitamin C ya sha, Alla ya bashi lafiya a tsawon jinyar da yayi na Coronavirus.
” An tambaye ni me na sha na warke, nace Chloroquine da Zithromax da Vitamin C likitoci suka rika bani har Allah ya bani Lafiya. Menene lai fin haka. Saboda haka ina nan akan baka ta cewa abinda na sha kenan.
“Idan mutum yana zazzabi, zai sha Chloroquine, idan cuta ce take damun sa zai sha Zithromax, idan ciwon kai ne zaka sha panadol, duk ba sai ka nemi izinin likita ba.