Yayin da cutar Coronavirus ke ci gaba da kashe rayuka da kassara tattalin arzikin kasashe, rage kudaden da Najeriya za ta kashe da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, zai iya samar da hanyoyin rage kashe kudade da kuma kudaden shigar da gwamnati ke tunanin samu a wannan mawuyacin yanayi.
Premium Times ta samu sahihan bayanan ayyukan da za a zabtare, a cikin wasu kwafe-kwafen takardun da suka fado hannun jaridar.
Rage kasafin kudin da gwamnatin Buhari ta yi ya zama dole, saboda annobar Coronavirus ta karya daraja da farashin danyen man fetur a duniya, wanda da shi ne kasar ke dogaro wajen samun kudin shiga.
Kasafin farko dai an yi shi a kan dala 57 kowace ganga daya, amma tilas ta maida kasafin a kan dala 30 kowace ganga.
Kiyasin Adadin Kudaden da Za a Rage: Takardun bayanan da suka fado hannun PREMIUM TIMES na yin nuni da cewa za a rage abin da ya kai naira bilyan 350 zuwa bilyan 1.5.
Wata wasika da Shugaban Kasa ya aike wa Ministar Harkokin Kudi Zainab Usman cikin watan Maris, ya ce, a fasa gudanar da duk wani aikin da muhimmmi ba ne ga kasa.
Kayayyakin Da Aka Fasa Saye:
An fasa sayen kwamfutoci, na’urar buga takardu, motoci bas-bas, taraktoci, babura, kayan alarun ofisoshi da na gidaje da sauran su.
Dama can jama’a da dama na cewa wadannan kayayyaki harkalla ce kawai ake yi, saboda duk shekara ana ware kudaden sayen su, amma kuma ba a ganin wadanda suka lalace.
Za a dakatar da daukar ma’aikatan gwamnatin tarayya, inda wannan zai shafi wadanda aka rigaya aka cika fam, irin su ‘Civil Defence, INEC da kuma Hukumar Kula da Shige-da-fice ta Kasa.
Za a zabtare kashi 16.7 na kudaden ayyukan yau da kullum na kowace ma’aikata da hukumomi, in banda fannonin tsaro, sojojin da bangaren kiwon lafiya.
“Duk wasu masana’antu na gwamnatin tarayya su zabtare kashi 25 bisa 100 na kudaden ayyukan su na yau da kullum da kuma kudaden gudanar da ayyuka, ko da kuwa Majalisar Tarayya ta rigaya ta amince da kudaden da za a ba su kafin hakan ta taso.”
An yi tafiyar ruwa da ayyukan raya masana’antu:
Wadannan dama ayyuka ne wadanda a kowace shekara ana yin kuka da su. Ayyuka ne da Mambobin Tarayya da Sanatoci ke cusawa a yi musu a kasafin kudi, amma kuma su ake bai wa kwangilolin, ko kuma su ke samo kamfanonin kwangilar. A karshe yawancin ayyukan ba yin su ake yi ba. Ko kuma a fara a bari, bayan an kwashe kudaden.
Wasu ayyukan ma sai biyu ake samun an biya kudaden su a wuraren da aka yi ‘yar-burum-burum a kasafin kudi.
Tsohuwar Ministar Harkokin Kudade ta nemi hana bayar da ayyukan mazabu ga ‘yan majalisa, saboda ta san abin akasari duk cuwa-cuwa ce. Sai dai ta kasa aiwatar da hana su kudin, saboda an same ta harkallar takardar NYSC ta bogi. Wa wannan Majalisar Dokoki suka rika juya ta kamar waina, saboda ta san sun san ta na da guntun kashi a cikin fatarin ta.
Sai kuma yadda Gwamnatin Buhari ta kama hanyar yin amfani da Rahoton Kwamitin Steve Oronsanye, wanda za a tattara hukumomin gwamnati masu yawan gaske a hade wuri daya. Hakan kuwa zai shafi wasu ma’aikata, musamman kanana.
Discussion about this post