CORONAVIRUS: Mutum 120,000 za su kamu a Legas nan da watan Agusta – Kwamishinan Lafiya

0

Gwamnatin Jihar Legas ta bayyana cewa har yanzu cutar Coronavirus ba ta kai kololuwar fantsama a jihar ba tukunna.

Kwamishinan Lafiya Akin Abayomi, ya ce sun yi kintacen cewa nan da watan Yuli zuwa Augusta cutar za ta kai kololuwar fantsama, inda ya yi hasashen cewa zuwa Augusta za a iya samun mutum 120,000 jimillar wadanda suka kamu da cutar a Jihar Legas.

Abayomi ya kara da cewa, “Idan aka yi nazari, daga ranar 7 Ga Afrilu, wata daya da ya wuce kenan, ana samun akalla mutum 10 sun kamu da cutar a kullum.

“Bayan makonni biyu kuwa sai aka rika samun mutum 32 na kamuwa a kullum. To yanzu kuwa har ta kai ana samun sama da mutum 100 a kowace rana.”

Hakan a cewar sa, har yanzu na a kai ga kololuwar fantsamar cutar ba, wadda ya ce sai Augusta ko Yuli za ta kai kololuwa.

Duk da haka ya ce Gwamnatin Jihar Lagos ta shirya domin aikin killace mutane da gwaji da kiyayewa.

Ya ce a yanzu haka da ake da masu cutar har 1491 a Lagos, ba don kwakkwaran matakan da jihar ke dauka ba, da yanzu yawan wadanda suka kamu sun kai 6,000.

A karshe ya ce za su ci gaba da aikin gwajin wadanda alamomin cutar suka fito ko suka bayyana a jikin sa.

Share.

game da Author