Kwamishinan Jihar Legas, Akin Abayomi, ya bayyana cewa sama da kashi 40 na wadanda ake samu da cutar a jihar, ba su yarda a gano takamaimen inda suke, tserewa su ke yi, ballantana a kai su a killace su.
Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar Juma’a, Abayomi ya ce wannan ne dalilin da ya sa ake ganin alkaluman wadanda suka kamu da ciwon a Jihar Lagos, amma kuma ga yawan gadaje birjik a cibiyoyin killacewa, babu masu cutar da yawa.
“Jami’an mu za su dauki samfurin gwajin mutum da adireshi da lambar waya. To yawancin wadanda gwaji ke nuna su na dauke da cutar, sai su tsere daga gidajen su, ba su yarda a je a dauke su a killace su.
“Wasu kuma ba adireshin gaskiya suke bayarwa ba. Sai jami’an mu au yi ta bilumbituwar neman su a cikin unguwa a rasa. Wasu kuma ka yi ta kiran lambar su su ki dauka, ko kuma idan su ka dauka, sai su rika yin kwatancen-gare, yadda ba za a iya gano inda su ke ba.”
Ba Mu Da Lokacin Farautar Masu Coronavirus:
Abayomi ya ce a yanzu ba su da lokacin farautar masu cutar a cikin gari. Abin da ke gaban su shi ne, su na gwada duk wanda suka ga ya na dauke da alamu cutar ne kawai.
Ya ce a halin yanzu kuwai gadaje 569, amma 307 babu kowa a kai. Ya yi kiran jama’a cewa duk wanda aka gwada ya kamu, to killacewa ita cw mafi sauki a wurin sa. Kuma ya ce wurin garas ya ke, an inganta shi, ba kamar lokacin cutar Ebola ba.
“Manyan jami’an gwamnati na kwanciya a wurin ana killace su, ana kula da su. Ko ni na kamu da a yanzu haka, a can za a killace ni.” Inji Kwamishina Abayomi.