Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 386 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Juma’a.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Juma’a, Jihar Legas ta samu karin mutum 176, 65-Kano, 31-Katsina, 20-FCT, 17-Borno, 15-Bauchi,
14-Nasarawa, 13-Ogun, 10-Plateau, 4-Oyo, 4-Sokoto, 4-Rivers, 3-Kaduna, 2-Edo, 2-Ebonyi, 2-Ondo, 1-Enugu, 1-Imo, 1-Gombe, 1-Osun.
Yanzu mutum 3912 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 679 sun warke, 117 sun mutu.
Jihar Kano ta samu karin mutum 65 ranar Juma’a. Jihar Katsina, Barno Bauchi da Abuja sun samu karin ywana wadanda suka kamu da cutar da dama.
Abu dai sai gaba-gaba ya ke yi a Najeriya, musamman jihohin Arewa da Legas.