Yaron da ake zaton ‘yan sanda sun harbe shi a Jigawa ya rasu

0

Wani yaro mai suna Usman dan shekara 10 da ake zaton ‘yan sanda suka harbe shi a Jigawa a kokarin tarwatsa gungun mutane a kasuwa ya rasu ranar Alhamis.

Mahaifin marigayi Usman, Abdulkadir Suleiman ya ce dansa wanda ke aji 5 a makarantar Firamare ya rasu a asibitin Kano.

Ana zaton ‘yan sanda ne suka harbe shi a lokacin da suke kokarin tarwatsa mutane a kasuwa a Sankara, Karamar hukumar Ringim, jihar Jigawa.

Daga asibitin Ringim ne aka tura su Asibitin Aminu Kano, domin a ci gaba da kula da shi. Allah yayi masa rasuwa ranar Alhamis.

Sai dai kum Rundunar ‘Yan sandan Jihar Jigawa, ta bayyana cewa ba jami’anta bane suka harbi yaron. Sun ce Ko da suka iso wannan kasuwa don tarwatsa mutane su bi dokar zaman gida dole, sai suka fara jefar su da duwatsu.

‘Yan sandan sun ce daya daga cikin duwatsun ne ya samu yaron a kai.

Share.

game da Author