Ahmed musa ya karyata rahotan wai ya kamu da Coronavirus

0

Fitaccen dan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya karyarta rahotan da ke ta yadawa cewa wai ya kamu da cutar Coronavirus.

Ahmed Ya bayyana cewa wannan labaran karya ne, cewada shi da iyalan sa lafiyan su lau.

Musa ya ce ya dawo daga kasar Saudi Arabia inda yake buga kwallon sa na kwararru a jirgin wadda daga shi sai iyalan sa. Kuma dukkan su lafiyar su lau.

Ya roki mutane da su yi watsi da wannan rade radi cewa labaran karya ne.

Share.

game da Author