Najeriya na shirin kwaso daliban kasar wadanda ke makale a Sudan sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus a duniya.
Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce dukkan daliban za a kwaso su ne kwauta, ba tare da sun biya ko sisi ba.
Tun da farko, Najeriya ta ayyana kwaso dukkan ‘yam kasar ta da ke makale a wasu kasashe, wadanda su ka kasa dawowa gida, saboda annobar Coronavirus.
Sai kuma sanarwar ta ce duk wadanda ke so a dawo da su Najeriya, to sai sun biya kudin tikoton jirgin dauko su zuwa gida.
Onyeama ya ce sai da gwamnati ta yi hakilon nemo kudaden da za ta kashe wajen maido daliban gida kyauta, bisa la’akari da cewa su kananan yara ne, ba wata sana’a su ke yi ba.
“Tilas ta sa mu ka fasa cewa su daliban sai sun biya kudi. Sai da mu ka nemo kudi da kan mu domin daukar dawainiyar dawo da su gida, da kuma nauyin killace su na kula da su tsawon kwanaki 14 idan sun iso Najeriya.” Inji Onyeama.
Sai dai kuma ya ce dalibai ne kadai za a yi wa wannan gatan ko alfarmar. Saboda karancin kudi, bai yiwuwa a ce a kwaso sauran jama’a a kowace kasa kyauta.
Discussion about this post