‘Yan sanda sun damke jigon APC da ya yi wa Minista kazafin kamuwa da Coronavirus

0

Baraka ta kara kunno kai a cikin shugabannin jam’iyyar APC reshen Jihar Enugu, bayan da ‘yan sanda suka yi cacukui da Shugaban Matasan APC na Shiyyar Sanatan Enugu ta Gabas.

An damke Nwojokun Okuyo bayan ya shiga soshiyal midiya ya yi kazafin cewa, “Ministan Harkokin Kasashen Waje Geoffrey Onyeama ya na dauke da cutar Coronavirus. An auna shi kuma an tabbatar. Shi ya sa ya je Enugu domin ya yada cutar cikin jama’a.”

An hakkake cewa wasu zaratan ‘yan sanda ne daga Ofishi ko Bangaren Musamman na Sufeto Janar su ka yi takakkiya har gidan mahaifin Okugo, da ke Oduma, cikin Karamar Hukumar Anniri suka damke shi, kuma har yau ba a bayar da nelin sa ba.

Shugaban bangare na APC na jihar Enugu, Ben Nwoye, ya ce Ministan Harkokin Kasashen Waje, wanda dan asalin jihar Enugu ne, shi ya sa aka damke Okugo.

Ya nuna takaicin cewa maimakon ministan ya yi amfani da mukamin sa a jam’iyya da kuma gwamnati ya samar da ci gaba a Enugu, sai ya ke amfani da mukamin sa ya na karfa-karfa da hauma-hauma a jihar sa.

Ya nuna mamakin yadda Mashawarci Kan Fannin Shari’a na APC na Jihar Enugu ya nemi a ba shi belin Okugo, amma ‘yan sanda suka ki bayar da belin, suka ci gaba da shi.

Sai dai kuma wani jigon APC a Enugu da ke bangaren ministan, ya ce babu ruwan Minista Onyeama da kamun da ‘yan sanda suka yi wa Okugo.

Ya ce wannan duk karairayi da sharrin yarfen siyasa ne. Sai dai kuma ya ce wani ne can ya rubuta wa ‘yan sanda korafi kan abin da Okugo ke watsawa a soshiyal midiya, wanda batunci ne ga wani ko kuma makusantan wanda ake batawa din.

Ya ce a kan wannan kuwa, daidai ne a kama shi, domin karairayi da sharri da kazafi mummuna da ya yi wa Minista Onyeama.

Share.

game da Author