Mahukunta a daya daga cikin manyan biranen Chana, Shenzhen, mai milyoyin al’umma, sun haramta cin naman kare da na kyanwa da ma na duk wasu namun dajin da a kan ajiye ana kiwo a cikin jama’a.
Wannan doka da birnin Shenzhen ta dauka za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga Mayu, 2020, kamar yadda gidan talbijin na CNN ya ruwaito.
An saka wannan doka ce domin guje wa sake barkewar mummunar cutar Coronavirus a Chana, wadda ta fara bulla a birnin Wuhan da ke cikin Gundumar Hubei.
An kuma haramta cin dabbobin da ake shiga jeji ana farauto su, ana sayarwa a cikin gari. Dokar dai za ta yi tsanani.
Dabbobin Da Aka Amince A Ci
Dabbobin da aka amince a rika ci a Shenzhen sun hada da: naman alade, naman shanu, tinkiya, naman jaki, zomaye, kaji, shanu, tantabaru, agwagwa da sauran su.
Hukuncin Karya Doka
“Duk wanda ya karya wannan doka, to hukuncin sa shi ne zai biya kudin dabbar da ya ci sau nunki 30, ko da dabbar ta kai Yen 10,000, wato daidai da dala 1400.”
Masana kimiyya da dama a Cibiyar Hana Cututtuka Yaduwa ta Chana, sun yi ittifaki da cewa cutar Coronavirus ta samo asali ne daga cin naman dabbobi.
Mahukuntan Shenzhen, sun ce wannan doka ta shafi duk wani mai sana’ar sayar da karnuka da maguna da sauran namun dajin da aka haramta ci.
An kuma hana kiwon dukkan wadannan dabbobi a cikin gida ko a wani garke ko ruga ko karkara.
Jami’an Shenzhen sun ce su na sa ran cewa sauran birane da gundumomi za su dauki wannan doka su yi amfani da ita, da nufin za a takaita harkokin yin riguna da fatun namun jeje da kuma dakile harkar masu kashe dabbobi su na yin magungunan gargajiya, ko man shafa da su.