Rundunar sojin Najeriya ta dakatar da karbar takardar neman yin murabus daga dakarunta.
Majiyar mu ta shaida mana cewa rundunar ta fitar da sanarwar tun a watan Maris ga duka sojin Najeriya.
Wannan umarni ya biyo bayan yadda daruruwan sojoji ke mika takardar yin murabus ga rundunar ne cewa sun gaji sun hakura da aikin sojin hakanan.
Duk da cewa ba a fadi yawan wadanda ke neman ajiye aiki ba ba idan aka kwatanta da yadda yake a da an samu cikakken bayanai cewa rundunar sojin ta dakatar da amsar irin wannan bukata daga duk wani sojin Najeriya.
” Guiwowin dakarun mu duk sun yi sanyi kan yadda aka yi watsi dasu, sai kashe su ake yi batare da shugabannin su sun yi wani abu akai ba. Musamman a wajen samar musu da kayan aiki masu nagarta kuma na zamani. Sannan kuma da halin ko in kula da manyan su ke yi musu a filin daga.
” Da yawa daga cikin wadannan sojoji sun dade a filin daga da Boko Haram, ba a canja su ba. Sai suka ga abin da ya fi dace wa su yi shine su hakura da aikin su koma ga iyalan su ko sa samu natsuwa su nemi wata sana’ar.” haka wani jami’in soja ya shaida wa PREMIUM TIMES a asirce.
Wani soja da ya rubuta wa shugaban rundunar sojin Najeriya Janar Tukur Buratai budaddiyar wasika ya bayyana cewa, ya gaji da aiki kuma yana bukatar ya ajiye aiki amma an ki amince masa ya ajiye aikin. Wannan Wasika ta karade shafukan yanar gizo.
Sai dai kuma wani babban lauya Abdul Mahmud, ya bayyana cewa rundunar sojin na da ikon kin amincewa da irin wannan bukata ta soja. Sai dai kuma dokar sojin ta ba ma’aikaci dama ya ajiye aiki idan ya gaji da ita.
” Doka ta ba rundunar soji daman kin amincewa da bukatar yin murabus daga aiki. Sai dai kuma shima ma’aikaci na da ikon ya nemi ajiye aiki idan ya gaji.”
Discussion about this post