Mahukunta a kasar Chana sun bayyana cewa ‘yan Afrika 111 aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus bayan gwajin cutar da akayi musu a garin Guangzhou.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta ruwauto haka ranar Talata.
A cikin wadanda suka kamu 19 sun shigo kasar ne da ita.
Idan ba a manta ba ‘Yan Afrika sun yi ta koka yadda mahukuntan kasar China ke wancakalar da su daga gidajen su da dakunan otel otel din su.
Hakan yayi matukar tada musu da hankali, da ya jawo har suka yi bore a kasar.
Sai dai kuma ma’aikatar harkokin kasashen wajen chana karkashin minista Zhao Lijian, ya bayyana cewa lallai sun samu rahotannin muzguna wa ‘yan Afrika. Amma kuma ana bincike akai.
Haka kuma kakakin majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamilla, ya nuna rashin jin dadin majalisar kan abinda ake yi wa yan Najeriya a kasar.