Coronavirus: El-Rufai ya saka hannu a saki bursinoni 76

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya saka hannun a saki bursinoni 76 dake tsare a gidajen kason jihar dake Kaduna da Kafanchan.

Sanarwar ta nuna cewa za a sallami bursinoni 73 daga gidan yarin Kaduna, uku a na Kafanchan.

Duk wadanda za a sallama sun kusa karkare zaman su a gidajen Yari.

Kwamishinan Shari’a ta jihar Aisha Dikko, ta bayyana cewa gwamnati ta yi haka ne domin a rage cunkoso a gidajen yarin domin kauce wa yaduwar coronavirus.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohi 20 da cutar ta bullo. Akalla akwai mutum shida da suka kamu da cutar a jihar, da gwamnan jihar Nasir El-Rufai.

A Najeriya kuma mutum 343 me suka kamu zuwa yanzu, sannan mutum sama da 100 sun warke.

Share.

game da Author