Yaki da Boko Haram na tafiyar Hawainiya, Yanzu zamu yi musu farad daya kawai – Inji Burutai

0

Babban Hafsan sojojin Najeriya Tukur Buratai ya bayyana cewa lallai yaki da Boko haram da sojojin Najeriya ke fama da na tafiyar hawainiya matuka.

Buratai ya ce yanzu lokaci yayi da zasu afkwa Boko Haram din domin kawo karshen su kwata-kwata a kasar nan.

” Za ku rika mamakin yadda wannan yaki da Boko haram ya dade ba a gama shi ba. Babban matsalar kuwa shine duk duniya ana samun matsala wajen yake da ta;\’addanci, wato ‘yan ta’adda. Muma matsalar da muke samu.

” Wasu kasashen ma sun yi fama da ta’addanci har na tsawon shekara 50. Amma na mu ba zai kai haka ba, zamu yi raga-raga da su nan ba da dadewa ba.

” Yanzu haka akwai wadanda muka saka suna samar mana bayanan sirri, kuma da zaran mun kammala kintsawa za mu afka musu kai tsaye mu tarwatsu kowa ya huta.

Sannan kuma duk manyan makaman da muka yo oda domin tun karar wadannan ‘yan ta’adda sun shigo kasar nan. Kuma shugabab Buhari na jinjina muku matuka. Nan ba da dadewa ba zamu kammala kintsawa mu ragargaje su kawai a gama komai.

Buratai ya dua wannan alkawai ni da yake ganawa da dakarun barikin Operation Lafiya Dole dake Ngamdu, jihar Yobe.

idan ba manta ba, ko a karshen wannan mako Boko haram suka afkawa wasu matafiya inda suka kashe mutum 7 sannan suka babbake kayan abinci da suka yi dakon su a garin Auno.

Share.

game da Author