Shin wadanda suka warke daga cutar COVID-19 za su iya sake kamuwa da cutar? Daga Dr Abdulaziz Bako

0

Masana suna kan bincike a kan cewa ko kwayar da ke kawo cutar COVID-19, wato SARS-COV-2, za ta iya kara bayyana a jikin wanda ya riga ya kamu da cutar ya warke.

A kasar Koriya ta Kudu (South Korea) akwai wasu mutane 91 da suka kamu da cutar suka warke amma sai aka sake gwada su aka ga suna dauke da kwayar cutar da ke kawo cutar COVID-19 wato SARS-COV-2. Babban abin tsoron shine kasancewar cewa wasu daga cikin wadanda suka warke daga (ma’ana an gwada su har so biyu babu cutar a jikinsu) sun sake dawowa da alamomin cutar COVID-19, an kuma sake gwada su an ga suna dauke da kwayar cutar SARS-COV-2.

Dalilan da za su iya jawowa irin wannan yanayin ya afku suna da yawa:

1 – Za ta iya yiwuwa an samu tangarda a wurin injina ko sinadaran gwajin cutar wanda zai iya sanyawa sakamakon gwajin ya kasance bai sahihantu ba.

2 – Za ta iya yiwuwa birbishin cutar ke ragewa a jikin mutanen da cutar ta kama suka warke, wanda idan hakan ne ana tsammanin ba lallai shi wanda ya warke din ya iya yada cutar ga sauran mutane ba (ma’ana, ba za’a iya yada cutar ta hanyar birbishinta ba)

3 – Tana iya yiwuwa kawayar cutar da ke kawo cutar COVID-19 tana labewa a wasu sassa na jikin wanda ta kama ta yadda bayan ya warke cutar za iya sake farfadowa. Idan hakan ta tabbata za mu iya cewa kamar kwayar cutar SARS-COV2 ta yi kamanceceniya da halayyar kwayar cutar da ke kawo abinda muke kira huciyar zazzabi (Herpes Labialis). Wannan kuma babban hatsari duba da zafin wannan cuta.

4 – Tana iya yiwuwa idan mutum ya kamu da cutar COVID-19 ya warke zai iya sake kamuwa da cutar ta hanyar cudanya ko mu’amala da masu dauke da cutar ko abubuwan da suka taba. Wannan shima zai kasance babban tashin hankali ga al’umar duniya idan ya tabbata. Domin hakan yana nufin cewa cutar za ta ci gaba da wanzuwa a cikin al’umma.

Daga karshe dai masana a kasar Koriya ta Kudu na kan bincike dan kokarin tantance dalilin da ya sa ake ganin alamun kamar wadanda suka kamu da cutar COVID-19 suka warke za su iya sake kamuwa da cutar. Ana sa ran sakamakon binciken zai fara fitowa nan da sati mai zuwa.

Share.

game da Author