Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya ce an fassara maganar sa ba daidai ba da aka ce ya ce bai san irin munin tabarbarewar bangaren lafiya a Najeriya ba, har sai da ya Shugaban Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus.
Mustapha ya yi wannan martani a ranar Juma’a a wurin taron ci gaba da yi wa just a karin haske kan irin ci gaban da kwamitin su ke samu a kullum.
Ya ce wannan kuma ba zai karye gwarin guyawun sa da shiga gaba domin a sake farfado da bangaren kiwon lafiya a kasar nan ba.
Sakataren gwamnatin ya ce shi cewa ya yi: “Aiki na a yanzu ya ba ni damar shiga sahun gaba domin a farfado da bangaren lafiya a kasar nan.”
Ya ci gaba da kare kan sa ya na cewa shi bai ce bai san halin tabarbarewar da fannin lafiya a kasar nan ke ciki ba.
“Wanda duk ke tunanin wai ban san irin lalacewar da fannin lafiya ya yi a kasar nan ba, to ya yin gurguwar fahimta. Domin na sani sarai.
“Ni din nan tantiri bakauye ne. A kauye fitik aka haife ni, shekaru 64 baya, inda ko asibiti babu, sai wani dan ofishin lafiya na sha-ka-tafi kadai.
“Shi kan sa dan ofishin sha-ka-tafi din wata mata ce unguwar-zoma ke kula da shi. Ko mai nakuda ba a kaiwa wurin ta haihuwa.
“Wannan ya sa ire-iren ko ranar haihuwar mu ba mu sani ba. Ba da ko katin shaidar ranar haihuwa. Sai katin rantsuwar-kaffarar-ikirarin shekaru kawai na ke da shi (declaration of age).
“Saboda haka na san halin da fannin kiwon lafiya ke ciki a kasar nan sarai. Kuma zan jajirce a sahun gaba domin na tabbatar an farfafo da tsarin kiwon lafiya a kasar nan.” Inji Mustapha.
PREMIUM TIMES HAUSA a ranar Juma’a ta buga labarin cewa, shekara biyar bayan hawa mulkin Shugaba Muhamadu Buhari, Sakataren Gwamnatin sa, Boss Mustapha ya bayyana cewa bai san bangaren lafiyar kasar nan ya yi mummunan tabarbarewa ba, sai kwanan nan, albarkacin nada shi da aka yi Shugaban Kwamitin Yaki da Coronavirus na Kasa.
Kafin Buhari ya hau mulki cikin 2015, ya yi alkawarin zai gyara fannin harkokin lafiya fiye da yadda yake a zaamnin jam’iyyar PDP.
Ya ce Gwamnatin APC za ta rika kashe naira 50,000 a kan kowane dan Najeriya domin kula da lafiyar sa.
Haka ya ke rubuce a cikin Kudirorin Jam’iyyar APC (APC Manifesto).
Idan ba a manta ba, bayan shekara uku da hawa mulkin Buhari, uwargidan sa Aisha ta cika da mamaki ganin yadda mo sirinji babu a Asibitin Fadar Shugaban Kasa, kamar yadda ta je kuma ta tabbatar da kan ta.
Shugaba Buhari bai taba zuwa wani asibiti a Najeriya damin a duba lafiyar sa ba, tsawon shekaru biyar kenan ya na mulki.
Duk ciwon jikin da ya ji, Ingila ya ke garzayawa ana duba shi, inda a cikin shekaru hudu ya shafe sama da kwanakin shekara daya a London ya na jiyya.
Duk wani mai hali ko baban jami’in gwamnati, kasashen waje ya ke zuwa ana duba lafiyar sa.
Da ya ke jawabi a gaban Majalisar Dattawa, Boss Mustapha ya ce, “Zan fada muku gaskiyar magana. Ban san fannin kiwo da kula da lafiya ya yi mummunar tabarbarewa ba sai yanzu.
“Amma akwai shiri na sha-yanzu-magani-yanzu da kuma na nan gaba Wanda za a yi domin ceto fannin harkokin lafiya a kasar nan.”
Sakataren Gwamnatin Tarayya ya kara da cewa za su yi taka-tsantsan wajen aiki da kudaden tallafin dakile Coronavirus da aka tara musu a bisa adalci ga kowace jihar kasar nan.
Kuma za a fadada wuraren gwajin cutar Coronavirus zuwa wasu jihohi baya ga wadanda ake kan ginawa a yanzu.
A na shi jawabi, Sanata Lawan Ahmed ya yi kira ga Kwamitin Yaki da Coronavirus ya yi amfani da kudaden da ake tara masa bisa ka’ida kuwa ta hanyoyin da suka dace.