Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kaduna Amina Bolani ta sanar cewa an gano wani mai gadi da ya kamu da cutar coronavirus a jihar.
Kwamishinan ta bayyana cewa mutumin ya shigo Kaduna daga jihar Legas dauke da cutar a jikinsa.
Wannan maigadi ya shigo jihar a motar haya wanda hakan ke nuna cewa ya yi cudanya da mutane da dama kafin ya iso Kaduna.
Kwamishina Amina ta ce tuni an aika da wannan mutum asibitin kula da masu fama da coranavirus sannan ma’aikatan kiwon lafiya sun fantsama domin gano gano mutanen da suka cudanya da wannan mutum tun daga Legas zuwa Kaduna da kuma wadanda ya cakudu da a Kaduna tun bayan dawowar sa.
” Babu wanda yasan adadin yawan mutanen da suka yi mu’amula da wannan mutum tunda dai motar haya ya shigo tun daga Legas zuwa Kaduna sannan ya fantsama cikin jama abin sa. na kwanaki yan harkokin sa kafin ya fara ciwo a gano daga baya coronavirus ce ya jijjibo.
A yanzu dai mutum 6 ne ke dauke da cutar a jihar.
Amina ta kuma ce gwamnati ta hana motocin haya da sauran ababen hawa dake jihar daukan mutane da yawa a domin hana yaduwar cutar.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne gwamnatin Kaduna ta sanar cewa daga 9 ga watan Afrilu, duk wani matafiyi a akasa ko a mota da ya gitto ta iyakar Kaduna, za a kama shi a ajiye a wajen killace masu fama da coronavirus na kwana 14.
Gwamnati ta saka dokar hana walwala a jihar Kaduna da kuma ratsawa ta jihar domin zuwa wata jiha domin hana had a cutar.
Sai dai kuma dokar zai bari wasu su rika wucewa idan suna da muhimmin uzuri na tafiya ko ratsawa ta jihar.
Manyan hanyoyin da aka hana bi ko ratsawa sun hada da Titin Kaduna-Abuja, Kaduna-Birnin Gwari, Kaduna-Zaria-Kano, Titin Kachia, Titin Bwari-Jere-KaAgarko, Titin Gumel-Kwoi-Keffi, Titin Zaria-Funtua da Titin Jos-Manchock.
Discussion about this post