• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba  sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad

    An yi amfani da ƴan daba ne aka kada ni – Bashir Ahmed

    Da Ɗan bindiga da ‘Deliget’, Ɗanjuma ne da Ɗanjummai – Shehu Sani

    ZAƁEN FIDDA GWANI: Fintirin Adamawa, Kashim ɗin Bauchi, Uban Makurɗi, Abachan Kano, Ashirun Kaduna sun yi nasara zaɓe na Jam’iyyar PDP

    Peter Obi ya fice daga PDP

    Peter Obi ya fice daga PDP

    TATTAUNAWA DA SARAKI:’Idan na zama shugaban ƙasa zan magance aringizon kuɗaɗen da ake yi wajen bayar da kwangiloli’

    Dino Melaye

    Dino Melaye ya sha ƙasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a Kogi

    EFCC ta cafke Okorocha bayan mamaye gidan sa da jami’an tsaro suka yi tun 11 na safe

    Dalilin da ya sa ƴan bindiga ke ci gaba da kai wa mutane hari a jihar Neja – SSG

    Yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 11 a Zamfara a karshen makon jiya

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

No Result
View All Result

KORONA BAROS: Tsumagiyar Kan Hanya, Daga Dr Nuruddeen Muhammad

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
April 1, 2020
in Labarai
0
Blood sample with respiratory coronavirus positive

Bayan na kammala duba marasa lafiya a wani yammaci, ban san lokacin da na tsinci kai na cikin tunanin irin sa’ar da na yi kasancewata cikin ƙoshin lafiya ba. A wani gefe kuwa na shiga yanayin tausayawa ga waɗanda Allah SWT ya ɗorawa larurar rashin lafiya. Babu abun tausayi a duniya kamar maras lafiyar da bai da d’an abun hannunsa da zai nemi magani, karma a ce rashin lafiyar ta kasance ta ko a mutuce ko a yi rai. Amma mu likitoci kan ci karo da ire-iren waɗannan matsaloli a kullum, musamman ma a asibitocin gwamnati. A takaice dai, babu fa wata sana’a da za ta sa mutum ya ga tsananin talauci da kuma sheda raɗaɗinsa kamar zama Likita a Najeriya. A asibitocinmune za ka ga bil’adama ya juya bayansa yayi tafiyarsa gida da tabbacin cewa mutuwa zai yi saboda kawai bai da Naira dubu ashirin (20,000) ko dalilinta! Haka dai Malam talaka a wannan ƙasa ke mutuwarsa ke kukansa shi kaɗai. Amma fa a inda gizo ya ke saƙar shine, idan dai ba wata kiyayewar Allah SWT ta musamman ba, toh fa su kan su shafaffu da man na daf da ɗanɗana kuɗarsu!

Cutur numfashi ta korona baros ta sako ɗan Adam a gaba. Annobar ta zama gagara badau, gobara daga kogi maganinki sai Lillahi, duba da yadda ta fara lallasa ƙasashen da suka fi kowaɗanne ƙarfi a duniya. Cutar, ta yi ɗiban karan mahaukaciya da ƙasashen da su ka yi fice a ƙarfin tattalin arziki, da ƙarfin makaman ƙare dangi, da ƙarfin tsarin kiwon lafiya, da kuma lafiyayyun al’umma. Korona baros dai ta zama tsumagiyar kan hanya, ki shafɗi babba ki shafɗi yaro, wadda ba ta ware bambamcin launin fata, ko ƙarfin arziki, ko kuma aƙida.

Ƙasashen yammacin turai da arewacin Amurka, da kuma ma su arziki na nahiyar Asiya sun kere sa’a wajen kula da mutanensu da kuma son more rayuwa. Sun ɗaukaki rayuwar duniya ta yadda babu abinda suke tsoro kamar barinta. Hakan ya sa suka tsunduma cikin duniyar kimiyya har ta kai da cewa ku san ba abun da ba su samo maganinsa ba sai dai mutuwar ita kan ta. Sun sa tsufa a gaba sai da suka rage masa gudu. Sun yi kutse cikin taswirar halittar ɗan adam (wato DNA) domin ƙera wasu daga cikin sassan jiki. Sun kuma yi tanade-tanade irin na gayawa jini na wuce domin yanayin rashin lafiya na gaggawa. Kyakkyawan misali shine; a yau a birnin New York na Amurka an kai matakin da duk wani kira na gaggawa daga ɗan ƙasa da bai samu ɗauki cikin kimanin mintuna tara da rabi ba to tilas hukomomi sai sun bi ba’asi sun kuma ɗauki mataki na ba sani ba sabo.

Amma mu anan Najeriya za a iya cewa rashin sani (wadda ake cewa ya fi dare duhu) a tsakankanin shafaffu da man mu ya sa su tunanin cewa za su iya yin baba na ɗaka gemu na waje. Bi ma’ana, su a na su ɗan ƙaramin tunanin, za su iya son ran su yadda su ke so anan gida Najeriya, amma kuma su tsallaka Turai domin su mori waɗancan tanade tanade na lafiya ma su inganci da su turawa su ka tsarawa ta su al’ummar. Ma su hannu da shuni dai sun mai da zuwa waje domin duba lafiyarsu ya zama jiki. A matsayinka na jami’in kiwon lafiya a ƙasarnan kuwa, dole watarana sai ka haɗu da wanda zai yaɓa ma ka irin wannan batu a fuskarka. Akwai yanayin raini da wannan mutane ke da shi; mai kamar cewa ni fa waɗannan asibitocin na ku ba irin nawa ba ne. Amma fa batun gaskiya anan shine: shin idan wani abu na gaggawa ya taso makwabta za’a naimo ko kuwa abokan hulɗa da ke can nesa? Da yawa harda waɗanda za su iya ɗaukar ɗawainiyar naiman lafiya a ko ina a faɗin duniya na mutuwa kullum a ƙasarnan ta silar bugawar zuciya da sauran makamantan cututtuka. Hakan na faruwane saboda ita dai bugawar zuciya ba ta jiran lokacin da ya wuce mintina talatin zuwa awa guda, ga shi kuma mu kwata kwata ba mu da wani tsari da k’warewa, da kuma isassun kayan aikin bada taimakon farko da kuma agajin gaggawa (emergency).

Babu wani abu da zai ƙara fallasa ainahin mummunan yanayin da harkar lafiyarmu ke ciki kamar wannan annoba ta Korona Baros. Ita dai wannan cuta idan tayi tsanani ta kan maƙure numfashin mutum ne, ta hanashi shan iska saboda lalata huhu da ta ke yi. A irin wannan yanayi kuwa kusan duk marasa lafiyar na buƙatar taimakon sinadarin iskar numfashi (wato oxygen). Wa su kuwa daga cikinsu har sai an kai ga ɗorasu akan injin numfashi na bentileto (ventilator).

Ita dai bentileto wata na’urar asibitice ta musamman mai taimakawa da numfashi wadda ke buƙatar likitoci na musamman (Anesthetics) domin sarrafa ta. Yau ƙasar Italiya ta shiga ƙarancin duka biyun, duk da kuwa cewa ƙasar na ɗaya daga cikin ƙasashe goma da su ka fi kowaɗanne ingancin tsarin kula da lafiyar al’ummarsu a duniya. Yanzu haka a arewacin ƙasar Italiyan, ƙwararrun likitocin da su kan su sun gajiya, ke yanke hukuncin wa zai rayu wa kuma zai mutu saboda ƙarancin na’urar bentileto.

Akwai dai darussa ma su dama da amafani ga Gwamnatoci da mu kammu ƴan Najeriya da ya kamata mu kiyaye daga wancan yanayi. Na farko dai dolene muɗauki dukkanin matakan kariya domin kare kawunanmu daga kamuwa da wannan cuta. Saboda da haka, abun a yabawa hukumomine, yadda mutanenmu da ke dawowa daga ƙasashen waje ke tabbatar da ingancin tsare-tsaren da aka tanadar a duk filayen tashi da saukar jiragen sama na Ƙasa da Ƙasa da mu ke da su a faɗin ƙasarnan. Amma fa akwai sauran aiki a gabanmu

Bijirewa gwaje-gwajen da aka tanadar a filayen jiragen da wasu mambobin majalisar tarayya su ke yi ba komai bane face nuna zallar rashin wayewa da ƙarancin sanin ya kamata a fili. Hakan misaline na irin tsantsar gadara da ƙafafa na wasu daga cikin shuwagabanninmu da ke kawo bala’in da kowama sai ta shafe shi. Shugaban ƙasa Muhammad Buhari yayi dai-dai da ya aikewa duka majalisun biyu da zungureriyar takarda dake gargaɗinsu akan waɗannan ɗabi’u.

Mu kuma ƴan Ƙasa a namu ɓangaren, dolene fa muzage dantse mu kiyaye dukkanin ƙa’idojin da masana da hukomomi su ke faɗa. Musamman ma na rage cinkoso, da yawaita wanke hannu, da kuma zama a cikin gida idan da damar yin hakan. Sannan kuma sai mu koma kan buzu domin yin addu’o’i da kuma tuba ga Ubangijinmu domin ya karemu daga wannan cuta, musamman ma irin nau’inta mai tsanani da kasashen Amurka da Italiya ke fama da shi.

Domin kuwa a duk faɗin Najeriya fa ba mu da wannan na’urar numfashi ta bentileto (ventilator) da ta wuce guda Ɗari Biyu kacal. Sannan su kan su ɗari biyun na tattarene a manyan manyan asibitocin da ke manyan birane irin su Lagos, Abuja, Ibadan, Kano, Zaria da Fatakwal. Idan ka ɗakko wannan matsalar sannan ka ƙarata akan matsalolin asibitocinmu na yau da kullum irin na rashin wadatattu da kuma ingantattun kayan aiki da gadajen kwantar da marasa lafiya, da kuma rashin ƙwararrun ma’aikata, za ka gane cewa idan fa wannan cuta ta sakomu a gaba (Allah ya kiyaye) kamar yadda ta saka waɗancan ma su jan kunnen, toh fa sai ɗan buzun mu! Bambamcin dai kawai shine, a wannan karon, yadda aka dama haka kowa zai sha. Domin kuwa waɗanda a da ke guduwa Turai domin neman lafiya yanzu babu gurin zuwa. Ai dama duk girman duniyarnan dai kowa ya san gidan ubansa; duk da kuwa ƙoƙarin cureta wuri guda da a ke ta faman yi. Zuwan Korona baros kuma ya ƙara tabbatar mana da cewa giji dai lahira ce, kuma na ka dai dole sai na ka!

Akwai ƙwararan darussa kuma marassa daɗi da za a samu bayan wannan iftil’ain ya wuce. Ala dole sai wannan gijin na mu mai suna Najeriya ya zauna ya nutsu ya kuma san inda kansa ke masa ciwo. Zuwan Covid 19 ya sa lafiya ta ƙara tabbatarwa da kowa a duniya cewa ita ce dai uwar jiki, wadda Mallam bahaushe ke cewa ‘sai da ke aka cin duniya, har ana ta marmari, har ana rawar jiki’. A saboda haka, ina da kusan tabbacin cewa duniya za ta zabura bayan wannan annobar. Za kuma ta shiga yin sabon shirin ko ta kwana – kamar yadda ta yi bayan barazanar nukiliya. Amma a wannan karon, za ta garzayane neman sabbin ilmin kiwon lafiya, da neman sani na musamman, da ƙirƙire – ƙirƙire da kuma uwa uba angiza magudan kuɗaɗe a gine ginen asibitoci da kayan aiki da horar da ƙwararru.

Mu ma dai a Najeriya dole mu shiga taitayinmu, mu kuma tsunduma a cikin wannan gudun yada kwarin wanin da za a yi domin tabbatar da cewa ba a ci gaba da barinmu a baya ba. Yanzu dai ya rage namu mu tattara hankalinmu a wuri guda, mu kuma farka, sannan musan ina muka dosa. Lokaci yayi da za muyi watsi da son zuciyoyinmu, mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar ɗai-ɗaikun banbance-banbance irin na siyasa, da ɓangaranci, da ƙabilanci dake tsakaninmu. A taƙaice dai, ba za mu taɓa iya tunkarar irin wannan ƙalubalen da ke gabanmu ba har sai mun zamto tsintsiya maɗaurin ki guda. A cikin irin wannan yanayi, tunanin cewa idan jifa ya wuce kaina toh ya fad’a kan uban kowa fa babban kuskurene. Tunda dai jifa irinna Korona ya nuna cewa zai iya yin kwana ya dawo ya fasa kan uban kowa ma!

Amma da yardar Allah SWT za mu ga bayan Korona Baros. Sai dai ya zama wajibi mu ƙudiri niyyar yin juyin juya hali a tsarin tunaninmu da kuma a aikace domin inganta harkar kiwon lafiyarmu. Domin ita fa harkar lafiya (ba ma ta Korona ba kawai) tamkar wata tsumagiyar kan hanyace, ta shafɗi Mallam Talaka ta kuma juya ta shafɗi Attajiri.

Nuruddeen Muhammad tsohon Ministane a Ma’aikatar Harkokin K’asashen Waje ta Najeriya.

Tags: AbujaBarosHausaKan HanyakoronaLabaraiNajeriyaNewsPREMIUM TIMESTsumagiya
Previous Post

CORONAVIRUS: Akalla mutane 40,000 sun mutu a duniya

Next Post

Dalilin da ya sa Coronavirus ta fi kashe maza fiye da mata – Bincike

Next Post
NCDC-CoronaVirus

Dalilin da ya sa Coronavirus ta fi kashe maza fiye da mata - Bincike

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • ZARGIN HARƘALLAR NAIRA BILIYAN 98: Bincike ba kaina farau ba, kuma kotun koli wanke ni ta yi – Amaechi
  • An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • El-Rufai ya lashe Zaben fidda gwani na kujerar majalisar tarayya, zai gwabza da Samaila Suleiman
  • An yi amfani da ƴan daba ne aka kada ni – Bashir Ahmed
  • Yadda ‘Ƴan bindiga suka sace fastocin cocin katolika biyu a Katsina

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.