Dalilin da ya sa Coronavirus ta fi kashe maza fiye da mata – Bincike

0

Yayin da duniya rankatakaf ke gaganiyar kokarin shawo kan cutar Coronavirus a duniya, alkaluman kididiga daga kasashe daban-daban da masana suka gudanar da bincike, sun tabbatar da cewa Coronavirus ta fi kashe maza da yawan gaske fiye da mata.

Farfesa Sarah Hawkes ta Cibiyar Tantance Jinsin Da Cuta Ta Fi Yi Kamawa da ke Birtaniya, ta bayyana cewa a baya fahimta ta tafi a kan cewa Coronavirus ta fi kamawa da kuma kashe dattawa da kuma wadanda ke fama da wasu cututtaka kafin barkewar Coronavirus.

Amma yanzu bincike ya nuna cewa Coronavirus ta fi yi wa maza rubdugun kwantarwa da kashewa.

Ga Dalilai

Bincike ya nuna cewa a farkon barkewar cutar a Chana, kashi 67 bisa 100 na wadanda suka kamu duk maza ne. Yayin da kashi 36 bisa 100 ne mata.

Wani bincike da aka tantance a kasashen Italy, Jamus, Koriya ta Kudu, Faransa da Spain duk ya tabbatar da cewa maza ne suka fi kamuwa, kuma su ta fi kashewa.

A Italy kashi 71 bisa 100 na wadanda ta kama duk maza ne, mata kuma kashi 29 bisa 100 kadai ta kama kuma ta kashe.

A kasar Spain mazan da suka mutu sun nunka mata, kamar yadda Farfesa Hawkes ta kara da cewa maza sun fi zaman barazanar mutuwa daga cutar Coronavirus, saboda yawan shan taba sigari da kwankwadar barasa fiye da mata.

Sannan kuma a Faransa an gano cewa daga ranar 1 zuwa 22, kashi 57 bisa 100 da suka kamu da cutar duk maza ne, kuma akasari dattawan da sun doshi shekaru 81 a duniya.

Hawkes da ba’arin wasu manyan masanan bin diggigin jinsin kamuwa da cututtuka sun kuma gano cewa mata sun fi maza karfafan kandagarkin kamuwa da cututtuka da makaran hana cuta rafke majiyyaci.

Sun ce maza sun fi saida rayukan su wajen yin ballagazar rayuwar shaye-shayen kayan da ke ragargaza kandagarkin jiki da kuma lalata musu kwayoyi da sinadaran hana cuta yin tasiri a jiki.

“Mace na da karfin sinadaran danne cuta da hana kwayoyin ta ragargaza makarai. Domin ko la’akarin yadda mace ke daukar ciki, ta raineshi tsawon watanni tara a jikin ta, to za a san lallai jikin mace na da makaran hana bakon abu yi mata luguden illoli da rafkewa. Jikin da wani sabon abu ya shige shi, kuma ya jure tsawon wata tara, ba kowace cuta ba ce za ta yi saurin ganin bayan sa.” Inji Farfesa Sarah Hawkes.

Coronavirus ta kashe mutane sama da 40, 000 a duniya. Kuma har yau ba a samo takamaimen maganin ta ko rigakafin kamuwa da cutar ba.

PREMIUM TIMES ta tattaro wannan bayani ne daga FRANCE 24. Kuma da iznin ta aka buga labarin.

Share.

game da Author