Bisa ga rahoton “Worldometer’ akalla mutum 800,000 sun kamu da cutar a duniya.
A ranar Asabar mutum 600,000 ne suka kamu. Zuwa ranar Lahadiabin ya kai 700,000.
Daga nan ne ya lula zuwa 803, 541.
A haka dai kuma an samu akalla mutum 172, 000 sun warke daga cutar a duniya.
ADADIN YAWAN MUTANEN DA SUKA MUTU A DUNIYA.
Bisa ga rahotanin da aka gabatar ranar Talata mutanen da suka mutu a dalilin kamuwa da cutar sun kai 40,000.
Kasashen Turai na cikin kasashen duniyan da suka fi yawan mutanen da suka mutu a dalilin kamuwa da cutar.
A kasar Italiya mutum 900 sun mutu sannan kasar Spain ta rasa mutum 800 a cikin awa 24.
A lissafe dai mutum 20,000 ne suka mutu a wadannan kasashe a biyu, wato Italiya da Spain cikin 40,000 da suka mutu.
Kasar Faransa ta rasa mutane 3000, kasar Birtaniya mutane 1400.
A ranar Talata mutane 3,305 sun mutu a kasar Amurka bayan mutane 500 sun mutu a kasar a cikin awa 24.
Likitoci sun yi hasashen cewa adadin yawan mutane da za su mutu a kasar Amurka zai kai 100,000 zuwa 200,000 koda mutane sun kiyaye dokar hana taro a kasar.
A garin New York mutane 67,000 sun kamu da cutar sannan mutane 250 sun mutu tsakanin ranar Lahadi da Litini.
Mutanen da suka mutu a garin sun kai 1,300.
NAHIYAR AFRIKA
Mutane 50 ne suka mutu a Nahiyar Afrika inda kasar Masar na da mutum 41, Algeria 35, Morocco na da 33.
Discussion about this post