Kin yarda da cutar coronavirus a Arewa, Jahilci ne ko Taurin kai? Daga Hawwa’u Alhassan

0

Duk da fadakarwar da ake ta yi a ko-ina a fadin Najeriya da yankin Arewacin Najeriya game da muni da illar cutar coronavirus, A yankin Arewa abin bai dada wasu da dama da kasa ba.

Za ak rika ganin wasu har alfahari suke yi da kamuwa da cutar. Babu abinda ya dame su. Sai kaga mutum yana yi mata gatse ko kuma yana karyata cutar ma kwata-kwata.

Wannan abu yana ci mana tuwa a kwarya matuka.

Kowa yana ganin yadda tattalin arzikin kasashen duniya da suka ci gaba da ta kasar mu, suka tabarbare. babu yadda za a yi. babu tafiya ko ina, kasuwanci sun tsaya cak, ana ta rasa ayyuka, sannan kuma wani na ganin duk haka ba gaskiya bane.

Kasashen da muke bugun kirji da su wajen kiwon lafiya duk sun dora hannu aka sun koka saboda wannan cuta. A najeriya gwamnati na kokarin ganin bai yadu zuwa ga karkara ba amma duk da haka mutane suna nuna halin ko in kula.

Lallai akwai abin tambaya a nan, Shin wai ko jahilci ne, Wayewa ne ko kuma taurin kai ne kawai na mutanen mu.

Jihohin Arewa da dama suna ci gaba da al’amurorin su babu abinda ya dame su.

Kokarin gwamnati shine, a iya dakile yaduwar wannan cuta. Amma wasu na ganin ba haka bane.

Mutum 10 sun mutu, sammam da 200 na nan a kwance a jihohi 20 a fadin kasar nan. Amma kuma duk da haka wasu na ganin aikin banza gwamnati take yi.

Wani ya nuna kansa a wani bidiyo wai gashi ya wanke hannu, ya kuma sha ruwan da ya wanke hannayen sa, babu abin da zai sameshi. Ba ya tsoron coronavirus. Ya je Legas ya ga yadda mutane ke kwance suna rokon Allah ya basu lafiya. Shi ya samu yana wa Allah tinkaho.

Don Allah ‘yan Arewa mu farga, mu tashi daga barci mu yi abin da ya kamata. Sannan mu ci gaba da rokon Allah, Allah yakawo mana saukin wannan Al’a mari.

Share.

game da Author