Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara kara wa’adin kwanakin zaman gida dole a Abuja, Legas da Ogun da Kwanaki 14.
Shugaba Buhari ya bayyana haka a jawabin da yayi wa ‘yan Najeriya ranar Litinin.
Buhari ya ce Gwamnati ta samar wa ma’aikatan aikin lafiya kayan kariya a wajen aikin. Sannan kuma ya jinjina musu kan aikin da suke yi.
Akalla mutum 323 ne suka kamu da coronavirus a Najeriya zuwa ranar Lahadi. Mutum sama da 80 sun warke sannan 10 sun mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar.
Idan ba a manta ba, shugaban Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnati ta saka dokar hana walwala garin Abuja, Jihar Legas da jihar Ogun makonni biyu da suka wuce.
Buhari ya ce dole a dakatar da shiga da walwala a wadannan jihohi da babban Birnin tarayya domin a iya dakile yaduwar cutar coronavirus a jihohin da Abuja.
Ya ce a wadannan lokaci babu wanda za a bari ya shiga wannan garuruwa ta sama ko kasa.
Bayan haka kuma za a biya masu karbar kudaden tallafi na tireda moni da kudin tallafi na manoma da kuma kudaden da ake ba gajiyayyu.
Bayan haka ya kara da cewa duk masu harkoki da ya shafi al’umma, kamar jigilar mai, abinci da harkarvwutan lantarki duk za su ci gaba da aiki.