COVID-19: Mutum biyu sun mutuwa a Legas

0

A ranar Talata ne kwamishinan kiwon lafiya na jihar Legas Akin Abayomi ya bayyana cewa mutum biyu dake dauke da cutar Covid-19 sun mutu a jihar.

Abayomi ya ce namiji mai shekara 45 da mace ‘yar 35 ne mutane biyu din da suka mutu a jihar.

A yanzu dai mutum 16 ne suka mutu a jihar legas.

Kwamishinan lafiya bai fadi ko a asibiti mai zaman kansa ne ko na gwamnati wadannan mutane biyu suka mutu ba.

Ya ce namijin dan kasar nan ne da ya dawo Najeriya daga kasar Indiya a watan Janairu 2020 ita kuma macen ta rasu ne a dalilin kamuwa da wasu cututtuka ban da coronavirus.

A yanzu dai mutane 379 ne ke dauke da cutar a jihar.

Daga ciki 260 na kwance a asibiti, 98 sun warke sannan 16 sun mutu.

Idan ba a manta ba sakamakon gwajin cutar da Hukumar NCDC ta fitar ranar Litini ya nuna cewa an samu karin mutu 38 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.

NCDC ta ce jihar Kano ta samu karin mutun 23, Kaduna 3, 5 a Gombe, Barno 2, Abuja 1, 1 a Sokoto, 1 a Ekiti.
Yanzu mutum 665 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 188 sun warke, 22 sun mutu.

Lagos-376
FCT-89
Kano-59
Osun-20
Oyo-16
Edo-15
Ogun-12
Kwara-9
Katsina-12
Bauchi-7
Kaduna-9
Akwa Ibom-9
Delta-4
Ekiti-4
Ondo-3
Enugu-2
Rivers-2
Niger-2
Benue-1
Anambra-1
Borno-3
Jigawa-2
Abia-2
Gombe-5
Sokoto-1

Jihar Kano dai tana ci gaba samun yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus. A sakamakon gwanjin ranar Litini, mutum 23 suka kamu da cutar.

Jihar Gombe, Sokoto da barno duk sun samu nasu rabon a ranar litini.

Jihar Kaduna ta samu karin mutum uku bayan ta sallami mutum hudu z makon da ya gabata. Gwamnan jihar Har yanzu bai sanar ko ya warke ko bai warke ba.

Share.

game da Author