Hukumar Kididdigar Alkaluma ta Kasa (NBS), ta ce farashin kayayyaki, wanda da su ne ake gane kuncin rayuwa ko yalwar arziki, sun nuna cewa kuncin rayuwa a Najeriya ya yi karuwar da bai taba yi ba tsawon watanni 23.
Ya zuwa watan Maris, an jera watanni bakwai a jere duk wata sai farashin kayayyaki sun tashi. Wannan kuwa na da nasaba da rufe kan iyakokin Najeriya da aka yi, sai kuma kulle garuruwa da aka yi a lokacin Coronavirus.
Rahoton Tashin Gwauron Zabon Farashin Kayan Masarufi ya tabbatar cewa an samu tashin farashi zuwa kashi 12.26.
Farashin kayan masarufi da abinci sun rika tashi tun.daga watan Satumba, 2019, bayan an rufe kan iyakokin kasar nan cikin watan Agusta, 2019.
Kulle kan iyakokin ya haifar da karin farashin shinkafa, man girki, abincin gwangwani nau’uka daban-daban da sauran kayan masarufi.
“Garkame Abuja, Lagos da Abuja ya haifar da tsayawar al’amurran aiki, sufurin kayan masarufi da sauran harkokin jigila da aikace-aikace.” Inji NBS.
Cikin watan Maris farashin kayayyaki ya haura da kashi 14.98 cikin watan Maris, a Bauchi, Neja, Bauchi, Kwara, Sokoto Abuja da Jigawa.
Har yau kokarin da Gwamnatin Tarayya ke ta yi don ganin ta rage radadin talauci da kuncin rayuwa a lokacin zaman zulumin kauce wa Coronavirus, bai yi tasiri ba.
Babban dalilin rashin yin tasirin, shi ne korafin da ake yi cewa kudade da kayan tallafin da ake rabawa, ba su isa wajen talakawan da ya kamata a ce su ne suka amfana, ko suka ci moriyar shirin.