Gwamnati jihar Kano ta bayyana cewa za ta mai da duk yaran makarantun allo dake jihar jihohinsu na asali.
Gwamnati ta Sanar da haka ne a wani takarda da kwamishinan yada labarai na jihar Muhammed Garba ya raba wa manema labarai ranar Litini a Kano.
Garba ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin rage yawan mutanen dake gararramba a titunan jihar.
Ya ce a kwanakin baya gwamnatin jihar ta rufe duk makarantun boko da na allo a jihar domin kare yara daga kamuwa da cutar coronavirus.
Ya ce almajiran ba su koma wurin iyayen su ba suna cunkushe a makarantun allon saboda rashin wuraren zama.
Garba ya ce gwamnati za ta hada hannu da sauran jihohi domin ganin ko wani almajiri ya koma gida wajen iyayensa.
Ga adadin yawan almajiran da za a maida jihohinsu na asali.
Katsina, 432
Yobe, 63
Kaduna, 198
Jigawa, 663
Bauchi, 101
Zamfara, 01
Gombe, 09
Nassarawa, 10
Kano (LGs), 117
Niger Republic, 01
Gwamnati ta yi kira ga mutane da su ci gaba sa kiyaye hanyoyin gujewa kamuwa da coronavirus tare da kiyaye dokar zama a gida dole da gwamnati ta saka.
Idan ba a manta ba a ranar 26 a watan Maris ne gwamnatin Jihar Kano ta bada umarnin cewa dukkan malaman makarantun allo da na tsangayu su rufe, a maida kowane almajiri gidan iyayen sa.
Gwamnati ta yi haka ne domin ta samu saukin dakile yaduwar tar Cornavirus a fadin jihar