CORONAVIRUS: Legas ba za ta iya jidalin kula da marasa lafiya 5,000 ba -Kwamishinan Lafiya

0

Gwamnatin Jihar Legas ta bayyana cewa idan cutar Coronavirus ta barke sosai fiye da yadda ba a samun masu ita yanzu sosai, to jihar ba za ta iya daukar dawainiya da jidalin kula da marasa lafiya 5,000 a cikin wata daya ba.

Wannan kakakusan gargadi ya fito ne daga bakin Kwamishinan Harkokin Lafiya na Jihar Lagos, Akin Abayomi, a lokacin da ya ke taron karin haske kan kokarin da jihar ta yi makonni biyu da suka shude wajen da kulawa da masu cutar Coronavirus.

A kan haka ne ya gargadi jama’a da su taimaki kan su da kan su, ta hanyar kiyayewa da bin ka’idar da likitoci da Hujumar NCDC suka gindaya.

“Idan wannan cuta ta barke bagatatan, to Lagos ba za ta iya kula da majiyyata akalla 5,000 a cikin wata daya.

“Kai wasu kasashen ma da dama su ma ba za su iya jekala-jekalar kulawa da wanann adadin ba.”

“Duk da ana samun raguwar masu kamuwa ba kamar yadda aka yi kirdadon samu da yawan gaske ba, duk da haka Abayomi ya ce kamata ya yi jama’a su kara yin taka_tsantsan da kiyaye ka’idoji

“Ana ta kokarin samun allurar da za ta warkar da masu dauke da cutar. Sannan kuma ana ta kokarin samar da kayayyakin kula da masu cutar.

A karshe ya ja kunnen jama’a su kiyaye kan su daga kamuwa da cutar Coronavirus, duk kuwa da cewa mutum 40, aka yi kirdadon cutar za ta kama. Ya ce wadanda ta kama zuwa yanzu haka a Lagos ba su fi mutum 120 ba.

Share.

game da Author