CORONAVIRUS: Mutum 6 sun kamu a Najeriya, yanzu 238

0

Mutum shida sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya, sanarwar hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ranar Litini.

NCDC ta ce sakamakon gwajin da ta yi ya nuna cewa an samu karin mutum 8 daga jihohi 3 da Abuja a kasar nan.

2 a jihar Kwara, 2 Edo, 1 a Ribas, 1 a Abuja.

Hukumar ta ce mutum 35 sun warke zuwa yanzu, 5 sun rasu.

Legas -120

FCT – 48

Osun – 20

Oyo – 9

Akwa Ibom – 5

Ogun – 4

Edo – 11

Kaduna – 5

Bauchi – 6

Enugu – 2

Ekiti- 2

Ribas – 1

Benuwe – 1

Ondo – 1

Kwara – 2

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), ta yi fatali tare da nuna rashin amimcewa da shirin da Najeriya ke yi domin gayyato likitoci daga Chana su zo taya kasar yaki da cutar Coronavirus.

NMA ta ce gayyato likitoci 18 zuwa Najeriya tamkar watsi da na gida ne, a kawo abin da ke nesa ne kawai.

Share.

game da Author