NAFDAC ta gargadi mutane su ankare da jabun maganin ‘Chloroquine’ da ya karade gari daga Chana

0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta na gargadin mutane su takatsantsan wajen siyan maganin zazzabin cizon sauro na chloroquine da ya karade kasuwannin Najeriya.

NAFDAC ta bayyana cewa an shigo da su daga kasar Chana ne kuma maganin duk ba masu kyau bane. Ya kan yi ajalin mutum ma.

Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ta sanar da haka ranar Litini tana mai cewa ta samu labarin magani ne a sako da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta aiko wa hukumar da shi.

Bisa ga wannam sako na WHO, kamfanin Jiangsu pharmaceutical Inc, Astral pharmaceutical New Bhupalpura, dake kasar Chana ne suke sarrafa kwayar maganin mai nauyin mg 250 guda 1000 a kwali.

Maganin kuma na dauke da lambar rajistar hukumar NAFDAC amma na karya ne 0587612. Sannan a yanzu haka an fara saida maganin har a kasar Kamaru.

A dalilin haka Mojisola ta yi kira ga masu shigo da magunguna da su daina shigowa da saida maganin a kasar nan.

Ta kuma ce hukumar za ta sala matakan tsaro a duk tashoshin jiragen ruwa da duk jihohin kasar nan da Abuja domin hana shigowa da maganin Najeriya.

Mojisola ta yi kira ga mutane da su gaggauta zuwa ofishin NAFDAC mafi kusa da su a duk lokacin da suka ga maganin a kasuwa ko kuma idan aka basu a dalilin rashin lafiya.

Ko kuma a kira wannan lambar waya 0800-1-NAFDAC da 0800-1-623322 domin shigar da kara.

Share.

game da Author