Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta nemi a kulle kowace jiha, a hana zirga-zirga daga wannan jiha zuwa tsawon kwanaki 14, domin a tsaida fantsamar cutar Coronavirus.
Cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ya fitar bayan ya sa ma ta hannu, ya ce akwai damuwa sosai ganin yadda cutar ke kara yaduwa cikin jihohin kasar nan, a dan kankanen lokaci.
Sannan kuma Gwamnonin sun ni a fadada aikin Dakile Cutar Coronavirus daga Gwamnatin Tarayya zuwa kowace jiha da kuma kowace Karamar Hukuma.
Ranar Labara ne Kayode ya fitar da sanarwa a madasmdin sauran gwamnonin kasar nan.
Daga kuma Ministan Lafiya, Ehanire ya nuna damuwa ganin yadda cutar ke kara yaduwa a cikin jihohin Najeriya.
Shi ma sai ya kara yin kira a kara tashi tsaye wajen yin duk abin da ya kamata ya yi a cikin gaggawa.
Gwamnonin sun nemi a kara inganta tsarin ayyukan Kiwon lafiya a matakin farko na kula da lafiya, a kananan hukumomi da sauran jihohi, ma’aikatu da ciboyoyi, domin a samu a yi wa Coronavirus korar-kare a kasar nan.
Sun ce idan aka hana zirga-zirgar jama’a daga wannan jiha zuwa waccan, hakan zai sa a rage yada cutar sosai.
Ya zuwa safiyar 23 Ga Afrilu, an samu mutum 873 da suka kamu da cutar, kuma ta kashe mutum 28.
Daga nan Gwamnonin sun bayyana cewa a wurin taron da suka cimma wannan yarjejeniyar, sun yi jimamin wadanda Coronavirus ta kashe, inda suka yi shiru ko tsit na tsawon minti daya.
Sun kuma yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ta’aziyya a kungiyance, ta tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.
Daga karshe kuma sun yi wa Gwamnan Kaduna, Nasiru Wl-Rufai barka da arziki, ganin cewa ya warke daga cutar Coronavirus, bayan killace kansa tsawon makonni hudu da ya yi.