Kungiyoyi 71 dake kasar nan sun yi kira ga gwamnati da ta janye dokar hana walwala a kasar nan. Kungiyoyin sun ce, mutane na matukar wahala sannan kayan abinci ya yi tsadar gaske.
Kungiyoyin sun ce maimakon ci gaba da garkame mutane, gwamnati ta ci gaba da wayar wa mutane kai ne shine ya fi.
” Idan ka shiga kasuwanni ko shaguna, kaya sun yi tashin gwauron Zabi, babu abin tabawa. Haka kuma motocin fasinjoji, kudin tafiya ya tashi matuka. Tallafi da gwamnati ta ke bada wa ba zai isa ba, ko kuma ma ba ya kaiwa ga mutane.
Bayan haka kungiyoyin sun koka kan yadda jami’an tsaro ke ta kashe ‘yan kasa a dalilin tabbatar da dokar hana walwala.
” Coronavirus ta kashe akalla mutum 28 amma jami’an tsaro sun kashe mutum 25. Wannan babban tashin hankali ne.”
Kungiyoyin sun yi kira cewa shawarar da gwamnoni suka dauka na sake garkamr mutane har na tsawon kwanaki 14, bai kamata a ya tabbata ba domin kuwa wuya za a sha.
Mutane da dama a jihohin Najeriya na kuka kan yadda gwamnati ta garkame mutane babu zirga-zirga. Hakan shine babban dalilin sa mutane ke fama da matsanancin yunwa a kasa.
A wasu jihohi kamar Bauchi, gwamnan jihar Bala Mohammed ya ce ba zai saka dokar Garkame mutane, ko zaman gida dole ba. Ya ce za a ci gaba da walwala sai dai mutane su kiyaye da cudanya cikin jama’a da kuma tsaftace kai.