Yayin da ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya ke cikin zaman kuncin fama da illar cutar Coronavirus, Jami’an Kwastan na Najeriya sun bada sanarwar damke kayan jama’a akalla na naira bilyan daya, daga watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara, wato Q1, ko kuma watanni uku na farkon shekara.
Wadannan makudan kudade na adadin kayan da aka kama ne a Shiyyar Zone B da ke Kaduna kadai, kamar yadda Shugaban Shiyyar, Mustapha Kebbi ya shaida wa manema labarai a Kaduna ranar Laraba.
Ya ce an kama wasu manyan ‘yan sumogal bakwai, kuma an kama kaya har sau 307.
“An kwace buhunan shinkafa 4,045, galan na man girki 1,416, kayan na taliya 1,915 da kuma dilar atamfofi da yadika 920.
An Kwace Bargar Motoci
A cikin wadannan watanni uku, kwastan sun kwace motocin jama’a guda 96, dila 322 ta hwanjo, babura 17, buhun wiwi 240 da sauran kayayyakin sa aka hana shigowa kasar nan da su.
Ya ce an kwace kayayyakin ne a kan iyakokin Kano, Katsina, Zamfara da Kebbi.
Ya kara da cewa wasu kayayyakin an kwace su ne a yanzu lokacin da aka killace hanyoyi ga garuruwa saboda Coronavirus.
Discussion about this post