Shugaban Gwajin Cutar Coronavirus na Kano, Nasiru Magaji, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa babu ranar da za a sake ci gaba da aikin gwajin cutar a Kano.
Da ya ke amsa tambayoyin jaridar, Magaji ya ce an sake bude dakin gwajin a ranar Juma’a, amma har yanzu ana ci gaba da shirye-shiryen da suka kamata a tsafatace dakin gwajin, kafin a sake ci gaba.
“Ka san an sake bude dakin gwajin a ranar Juma’a, amma a gaskiya ba a ci gaba da aikin gwajin ba tukunna, saboda sai an yi wasu shirye-shirye da kimtse-kimtse.”
Magaji ya ce an aikin yi wa dakin gwajin feshin tsarkake shi, wanda abu da zai dauki kwanaki biyu, wato awa 48.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga cewa daga mambobin aikin gwajin mai suna Isa Abubakar, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an dakatar da aikin gwajin ne saboda rashin kayan aiki.
Sai dai kuma a ranar Alhamis ne Ministan Harkokin Lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an dakatar da gwajin masu cutar Coronavirus a Kano ne saboda wasu masu gwajin sun kamu da cutar a dakin da su ke yin gwajin.
Ehanire, wanda ya yi wannan bayanin da yammacin Ladaba, ya ce an kuma fuskanci karancin sinadarai da kayan aikin gwajin, wanda hakan ya sa tilas aka dakatar na wani dan takaitaccen lokaci.
“Rahotanni sun tabbatar an samu karancin kayan aiki musamman kayan kariyar da jami’an kiwon lafiya ke sakawa da daurawa. Kuma an samu karancin wasu sinadarai. Amma dai a yanzu duk mun tura musu kayan.
“Wasu masu aikin gwajin sun kamu a dakin da ke yin gwajin. Hakan ya sa tilas aka gaggauta rufe dakin gwajin, daga baya aka je aka yi masa feshin tsarkakewa daga. cutar Coronavirus.”
Ehanire ya ce rufewar ta wani dan takaitaccen lokaci ce, kuma tuni an ci gaba da aikin gwajin, saboda an aika musu da dukkan kayan aikin da ake bukata.
PREMIUM TIMES ya tabbatar da cewa ana a cikin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ake gwajin a wani dakin gwajin cututtuka (laboratory).
Can ne kuma ake kai gwaje-gwaje ana aunawa da jihohin Arewacin kasar nan da dama.
Halin Da Kano Ke Ciki:
A ranar Asabar birnin ya rude, ganin yadda aka rika watsa bayanan mashahuran mutanen da suka mutu a rana daya a Kano.
Cikin wadanda suka mutu har da Farfesa Ibrahim Gambari, wanda ya yi wa tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo Shugaban Kwamitin Inganta Tattalin Arziki.
Gambari shi ne shugaban mashahuriyar sakandare mai zaman kan ta ta Kano, wato Makarantar Hassan Gwarzo da ke Sallare, Kano.
Akwai kuma tsohon Editan Leadership Sunday, Tijjani Abubakar da wani Farfesa, da ke koyarwa a Jami’ar Bayero sai kuma mahaifiyar dan wasan barkwanci, Ado Gwanja.
Rasuwar wadannan mutane sama da 12 ta haifar da surutai a soshiyal midiya, inda ake ta kiran Shugaba Muhammadu Buhari ya karkato ya dubi halin da Kano ke ciki, kamar yadda ya ke maida hankali ha Lagos.
Wasu kuma na kira da a maido Kwamitin Yaki da Coronavirus daga Abuja ya dawo Kano, zuwa wani dan lokaci, domin a shawo kan halin da al’ummar Kano ke ciki.
Masu irin wannan ra’ayin har da Farfesa Yusuf Usman, tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiyar Ma’aikata.
Yusuf ya ce halin da Kano ke ciki zai iya shafar Arewa baki daya, Najeriya da ma makwautan kasashe.
Sannan ya shiga sahun wadanda suka ragargaji Gwamna Abdullahi Ganduje wajen yin sakaci da suka siyasa a lamarin yaki da cutar Coronavirus.
Akwai kuma masu ganin cewa Ganduje ya yi babban kuskure da ya bude kasuwanni a ranar jajibirin fara azumi. An ce kasuwancin Kano sun yi cikar da ba su taba yin irin ta ba a ranar Alhamis da ta gabata.
Yawan mace-macen da ake yi Kano na karuwa, duk kuwa da cewa Ganduje ya shiga gidan talbijin na Channels ya karyata adadin da jaridar Daily Trust ta buga cewa an rasa a cikin makon da ya gabata.
Yawan wadanda suka mutu a ranar Asabar ya sa an ci gaba da ragargazar Ganduje, ana cewa ba zai iya jagorantar aikin dakile cutar Coronavirus a Kano ba.
Jama’a da dams kuma na nuna rashin amincewa da bai wa kwamitin da Ganduje ya kafa amanar ceton rayukan al’umma.