Masu garkuwa sun yi awon-gaba da ‘ya’yan wani mashahurin mai wa’azin addinin Musulunci a garin Badun, babban birnin jihar Oyo.
Masu garkuwar sun ritsa ‘ya’yan Akawugbagold da bindiga, suka karkada su a cikin mota suka arce da su.
Da ya ke bayani a shafin sa na Facebook, inda har hotunan ‘ya’yan na sa ya saka, malamin ya ce an yi garkuwa da ‘ya’yan na sa wadanda tagwaye ne, mace da namiji a ranar Asabar da karfe 8 na dare, a lokacin bayan ya bar gida kenan ya yi rikodon na tafsirin da ya ke gabatarwa.
Ya roki jama’a su taya shi addu’a Allah ya kubutar da ‘ya’yan na sa, mace da namiji, wadanda ya ce a halin yanzu mahaifiyar su ta shiga wani mawuyacin hali tun bayan tserewa da yaran da aka yi, wadanda ya ce Allah ya albarkace ta da su bayan shekara 12 da aure, sannan ta haife su.
Ya roki jama’a su taya shi roki da lallashin masu garkuwar su dubi girman Allah su saki yaran.
Kakakin Yada Labaran Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo, Fadife, ya tabbatar da sace yaran. Ya ce sun samu rahoton, har ma sun yi kamun wasu da ake zargin da hannun su.
Cutar Coronavirus ba ta hana masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga da Boko Haram ci gaba da kai hare-hare ba a kasar nan.
Farkon makon da ya gabata mahara sun kashe mutum 47 a Karamar Hukumar Safana da kewaye ta jihar Katsina.
Discussion about this post