Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta kwashi almajirai 1098 ta maida su jihohin su na asali. Haka dai Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar, Murtala Garo ya shaida wa manema labarai a Kano.
Garo ya ce an maida wasu sama da 400 a Katsina, sama da 500 a Jigawa, wasu kuma a wasu jihohin.
Kano ce birnin sa ya fi cinkoson kananan yara wadanda ke barace-barace ba tare da zuwa makaranta ba.
Akalla an kiyasta akwai sama da yara milyan 10 da ba su zuwa makaranta, kuma akasarin su a Arewa su ke.
Gwamnatin Kano ta ce dukkan almajiran 1098 da aka kwashe, sai da aka yi musu gwajin cutar Coronavirus, amma ba a samu ko daya da ita ba.
A na ta bangaren, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce duk da Kano ta yi ikirarin yi wa almajiran sama da 500 gwaji, to wannan ba zai hana jihar ta killace su wuri daya har tsawon kwanaki 14 ba, sannan ta sallame su.
Jama’a da dama na tababar yi wa almajiran gwaji da gwamnatin Kano ta yi ikirari, musamman ganin cewa tun cikin farkon makon da ya gabata aka kulle dakin gwajin cutar Coronavirus da ke cikin Asibitin Aminu Kano, bayan da wasu masu gwajin da jami’an kwamitin yaki da cutar suka kamu.
Da dama kuma na ganin laifin gwamnatin ganin yadda ta kwashi almajiran a daidai lokacin da ake dama da cuta, ta watsa su cikin wasu jihohi.
Sannan kuma akwai masu ganin cewa babu abin da hana almajiran komawa Kano, domin babu wata hanyar da aka dauka da za a iya hana su sake shiga birnin, wanda a yanzu cutar Coronavirus ta fantsama sosai a ciki.
Akwai rahoton mutum 77 da suka kamu a jihar Kano. Sai dai kuma ana ganin adadin ya zarce haka nesa ba kusa da, idan aka yi la’akari da yadda aka dakatar da gwajin cutar Coronavirus a jihar.
Sannan kuma yawan mace-macen da ake yi birjik a Kano ya kara jefa fargaba a kasar nan cewa ba a ma san iyakar adadin yawan wadanda suka kamu da cutar a Kano ba.
Discussion about this post