CORONAVIRUS: A damke Abba Kyari a daure shi saboda sakaci da ganganci -Guru Maharaj Ji

0

Shugaban addinin hululun zamani, Guru Maharaj Ji da ke Lagos, ya shawarci ‘yan Najeriya cewa gara ma su kama dahir, amma abin da ya kira surkullen addini ba ya maganin cutar Coronavirus.

Da ya ke ci gaba da bayani a taron manema labarai a Legas, Maharaj Ji ya yi kira a gurfanar da Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.

Ya ce bai ga dalilin da zai fita kasar da ya san ta na fama da cutar Coronavirus ba, sannan kuma da ya dawo gida Najeriya bai killace kan sa ba. Sai ya rika shiga jama’a ya na mu’amalolin sa.

Maharaj Ji ya ce, “shin wannan keta ce ko mene ne? Me ya taka ne, me ya ke nufi kuma shi wane ne?”

Mutane da dama tun a farkon bullar Coronavirus a kasar nan sun nuna bacin rai ganin yadda Kyari ya ki killace kan sa bayan ya dawo daga Jamus, sai ma ya rika fita ya na wasu harkoki, kuma ya ci gaba da shiga taron danawa da manyan jami’an gwamnati.

Bayan haka ya yi suka ga addinan Najeriya cewa gara ma kowa ya watsar da wani addini ya bi Sat Guru Maharaj, Shugaban ‘One Love Family.

Kuma ya ce sanin wane ne mahalicci shi ne addini, ba wai a shiga coci-coci surkullen kiraye-kirayen abin da kai da kan ka ma ba ka san abin da ka ke fada ba.

Ya ce gara ma tun da wuri ‘yan Najeriya su kama turbar kiran sunan mahalicci, ba hauragiyar soki-burutsun da ake yi a coci-coci ba.

“Ta ina za ka samu tsira alhali ka takarkare ka saki sunan mahaliccin ka na kiran abrakadabra?

Ka sani wata Holy Spirit ko holy Micheal da holy fire, duk ba za su yi maka magani ba. Ka nemi ilmi na hakika, domin da ilmin hakika ake ma sanin mai Coronavirus.

“Ai ga shi nan ‘yan Holy Gost Fire duk sun tsere, sun yi tsit. Mun daina jin ana ‘Praise the Lord. An ma rufe wasu muhimman wurare a Makka da Madina.

Share.

game da Author