CORONAVIRUS: An gurfanar da Fastoci biyu da suka karya doka a Kotu a Kaduna

0

Gwamnatin Kaduna ta gurfanar da wasu Fastoci biyu da suka karya dokar Hana gudanar da taro da gwamnatin jihar Kaduna ta saka.

Fastocin biyu masu suna Ifeanyi Ojonu da Giniki Okafor sun gudanar da taron bauta a coci da mabiyan su a unguwar sabon Tasha ranar Lahadin da ya gabata.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya bayyana haka a jawabi da yayi wa manema labarai a jihar Kaduna.

Aruwan ya ce gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen tabbatar da bin doka da oda fadin jihar.

Idan ba a manta ba a makon jiya, gwamnati ta damke wasu limamen masallacin Juma’a biyu a Malali da Unguwan Kanawa da suka karya doka irin haka.

Suma an garzaya da su kotu domin hukuntasu bisa karya doka da suka yi.

Jihar Kaduna na da akalla mutane 5 yanzu da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus da yanzu haka suna kwance ana duba su.

Cikin su har da gwamnan jihar, Nasir El-Rufai da shine mutum na farko da ya kamu da wannan cuta a jihar.

Share.

game da Author