CORONAVIRUS: Saka dokar hana walwala a Kaduna da Abuja alheri ne ga mutane

0

Kamar yadda aka sani daya daga cikin hanyoyi kamuwa da cutar coronavirus shine ta hanyar cudanya da wanda ke dauke da cutar.

Sai dai kuma likitoci sun bayyana cewa ba za a iya gane alamun cutar a jikin mutum ba da ido har sai bayan kwanaki 14.

Likitoci sun ce a tsakanin wadannan kwanaki mai dauke da cutar zai iya yadawa mutane sama da 10 ta hanyar cudanya, Ko idan ya yi tari ko atishawa ba tare da ya sani ba.

Ganin haka ne gwamnati ta kafa dokar hana walwala domin hana yada cutar musamman yadda kasar ke fama da fannin kiwon lafiya dake gab da rugujewa.

Saka dokar dai ya zama alheri ga mutane domin ya taimaka wajen kare mutane daga kamuwa da cutar musamman mazauna karkara.

Sai dai da dama musamman talakawa ba za su ga alherin haka ba ganin sai sun fita ne sannan suke samun na ci da sha a gidajen su.

Idan da an bar mutane sun ci gaba da harkokinsu na shiga da fita da komai ya kicame domin a yanzu haka mafi yawan mutanen dake dauke da cutar a kasar nan mutane ne da suka dawo daga kasashen waje.

Sannan a dalilin haka wasu mutane mafi kusa da masu dauke da cutar ke kamuwa saboda cudanyar da suka yi da su.

Domin samun nasarar dakile yaduwar cutar gwamnati ta yi kira ga mutane da su bi dokar hana walwala da ta saka sannan a Yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu tare da tsaftace muhalli domin samun kariya.

Idan ba a manta ba a ranar 20 ga watan Maris ne Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da hana manyan gangami, tarukkan bauta a Coci-coco da salloli a masallatai.

Sannan a Lahadin da ya gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka dokar hana walwala a garin Abuja, Jihar Legas da jihar Ogun.

Gwamnatin tarayya da gwamnati jihar Kaduna sun saka dokar hana walwala domin hana yaduwar cutar coronavirus.

Bayan haka gwamnati ta hana Jami’anta fita zuwa kasashen waje sannan ta hana tashi da saukan jiragen sama a kasan duk domin hana shigowa da cutar kasar nan.

Sai dai duk da haka cutar ta shigo kasar ta kuma yadu zuwa wasu jihohin dake kasar nan.

A yanzu mutane 238 ne ke dauke da cutar.
35 sun warke sannan biyar sun mutu a kasar nan.

Cutar ta bullo a jihohi 13 a kasar nan sannan jihar Legas ce jihar da ta fi fama da cutar a kasar nan.

Share.

game da Author