Azumin Ramadan: Matsayi Da Falalarsa A Musulunci, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahamah, Mai Jin Kai

Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mabuwayi, tsarkakakken Sarki. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyyayyan halitta Annabin karshe Annabi Muhammad (SAW), da alayensa da sahabban da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Ya ‘yan uwana masu girma, kamar yadda kuka sani, watan azumin Ramadan shine wata na tara a lissafin watannin Musulunci guda goma sha biyu, kuma a cikin sa ne Musulmi a duk fadin duniya suke gudanar da Ibadar azumi na tsawon kwanaki ashirin da tara (29) ko talatin (30).

Wannan wata mai daraja yana dauke da dimbin falala da albarka da rahamar Ubangiji Subhanahu Wa Ta’ala. Don haka yake da muhimmanci ga al’ummar Musulmi, su gudanar da ayukkan Ibadah da neman lada don samun gafara da rahamar Allah Madaukakin Sarki.

Bugu da kari, watan Ramadan yana dauke da muhimman abubuwa na tarihin addinin musulunci masu tasiri a rayuwar Musulumi baki daya. Wannan a takaice kenan.

Ma’anar azumi da lokacin wajibcin sa: Ma’anar azumi a yaren larabci shine: “Kamewa”, amma a Shari’ance azumi shine: “Kamewa da niyyar bauta, daga barin ci da sha da saduwa da iyali da kuma sauran abubuwa masu karya azumi, daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.”

Tarihin wajabta azumi: Allah madaukaki ya wajabta shi ne ga al’ummar Annabi Muhammad (SAW) kamar yadda ya wajabta shi ga sauran al’ummomin da suka gabata, domin fadin sa Allah madaukakin Sarki:

“Ya ku wadanda suka yi imani! an wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku,
tsammanin zaku samu takawa.” [Suratul Bakarah: 183]

Kuma wannan ya kasance ne a watan Sha’aban, a shekara ta biyu bayan hijrah.

Fa’idodin azumi: Azumi yana da fa’idodi na zuciya, zamantakewa, da na lafiya. Sune kuma kamar haka:

– Daga cikin fa’idar azumi ta zuciya (wato ruhi): shine yana taimakawa wurin samun hakuri da juriya, da kuma karfafuwa a kan haka. Sannan yana samar da kamewar kai da kuma taimakawa kai, haka kuma yana samar da kiyaye zuciya daga sabawa Allah mai girma da daukaka da kuma dora ta akan tarbiyyar hakan.

– Daga cikin fai’dar zamantakewa kuwa, azumi yana sabarwa mutane tsari da kokari, da son adalci da daidaituwa akan gaskiya, kuma yana kimsawa mumini tausayi da dabi’u masu kyau, kamar yadda mutane ke kamewa daga sharri da kuma abin da yake barazana ne.

– Daga cikin fa’idar sa shine samun lafiyar jiki: azumi yana tsarkake kayan ciki, kuma yana gyara hanji, yana kyautata jiki daga kamuwa da cututtuka kuma yana tsane jiki daga yawan mai (kitse) da nauyin jiki.

Tabbatar da kamawar watan Ramadan: Shigowar watan Ramadan yana tabbata ne da dayan lamari biyu:

Na farko: Cikar watan da ya gabace shi (kwana talatin) wato Sha’aban. Idan Sha’aban ya cika kwana talatin, rana ta talatin da daya yini ne na Ramadan kai tsaye.

Na Biyu: Ganin jinjirin watan Ramadan. Idan aka ga jinjirin watan Ramadan a daren talatin na wannan wata. Domin fadin Allah madaukakin Sarki:

“Duk wanda ya shaidi (shigar) watan Ramadan to ya azumce shi.” [Suratul Bakarah: 185]

Haka kuma da fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

“Idan ku ka ga jinjirin wata to kuyi azumi, kuma idan ku ka gan shi ku ajiye, idan kuma an boye maku shi ta (dalilin giragizai) to ku cika shi talatin.” [Bukhari da Muslim]

Idan mutanen wani gari suka ga watan azumi ya wajaba gare su. Kamar yadda yake fitar wata yana sabawa, misali fitar wata a yankin Asiya daban yake da yadda fitar shi take a yankin Turai da Afrika ba haka yake ba a latin Amirka misali. Da haka ne ko wane yanki da bangare na duniya suke da hukuncin da ya kebance su game da ganin wata. Idan kuma al’ummar musulmai baki daya suka yi azumi da ganin wata daya to wannan shine abin da yafi kyautatuwa da bayyana hadin kai da kuma ‘yan uwantaka.

Ganin watan mutum daya adali ya wadatar ko mutum biyu, kamar lokacin da Manzon Allah (SAW) ya halasta ganin watan mutum daya na Ramadan (Muslim ne ya ruwaito shi). Amma na ajiye azumi (wato watan Sallah) sai da ganin
adilai biyu, kamar yadda Manzon Allah (SAW) bai halatta ganin wata na adili daya ba a lokacin ajiye azumi.

Wajabcin Azumin Ramadan: An wajabta azumi a cikin Alkur’ani ne da Hadisai da kuma Ijma’in malamai, kuma azumi daya ne daga cikin rukunnan musulunci. Allah Ta’ala yace:

“Watan Ramadan shine wanda aka saukar da Alkur’ani a cikin sa, yana mai shiyarwa ga mutane da kuma bayyanar da shiriya da kuma bambancewa (tsakanin karya da gaskiya), to duk wanda ya shaidi watan daga cikin ku sai ya azumce shi…”. [Suratul Bakarah: 185]

Kuma Manzon Allah (SAW) yace:

“An gina musulunci ne akan abubuwa guda biyar: Shaidawa da babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, da tsaida Sallah, da bayar da Zakkah, da ziyartar daki (wato Hajji), da kuma azumin watan Ramadan.” [Bukhari da Muslim]

Rukunnan Azumi: Azumi yana da rukunnai kamar haka:

1. Niyyah: Ita ce kuduri a cikin zuciya akan kamewa domin bin umarnin Allah, da neman kusanci zuwa gare shi, domin fadin sa:

“Dukkan aiki na Ibadah sai da niyyah …..” [Bukhari da Muslim]

2. Kamewa: Shine nisantar duk wani abin da zai
karya azumi na ci ko sha ko saduwa.

3. Lokaci: Abin nufi shine yini, shine kuma daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.

Sharuddan wajabcin Azumi: Sharudan wajabcin azumi guda hudu ne kamar haka:

1. Musulunci

2. Balaga

3. Hankali

4. Iko

Sannan kuma sharadi ne mace ta tsarkaka daga jinin al’ada da jinin haihuwa.

Sharuddan Ingancin Azumi, sune kamar haka:

1. Musulunci

2. Daukar niyyah da dare

3. Wayo

4. Yankewar jinin al’ada

5. Yankewar jinin haihuwa (wato jinin biki)

Sunnonin Azumi:

1. Gaggauta bude baki, shine kuma bude-baki da zarar an tabbatar da faduwar rana.

2. Abin bude baki ya kasance danyen dabino ko busasshen dabino ko kuma ruwa, wanda yafi a cikin ukun nan shine na farko da na karshe kuma shine na karshen su, mai bi masu kuma shine na biyun, an so a bude baki da wutiri, (wato mara).

3. Addu’a yayin bude baki: Manzon Allah (SAW) ya kasance yana cewa a lokacin bude-bakinsa:

“Ya Allah don kai muka yi azumi, kuma da arzikin ka muka bude baki, saboda haka ka karba muna. Lallai kai ne mai ji kuma masani.” [Abu-Dawud]

4. Cin sahur, har zuwa karshen dare, da niyyar azumi.

5. Jinkirta sahur, har zuwa tsagin dare na karshe.

Abubuwa Abin Kyama Ga Mai Azumi: An karhantawa mai azumi wasu al’amurra wadanda ke iya jawo lalacewar azumi, amma da yake su a karankansu ba sa karya azumi kai-tsaye, sune kamar haka:

1. Kai makura wurin kurkurar baki da shaka ruwa a hanci lokacin alwala.

2. Sumbata, ita tana tasiri ta janyo sha’awa wadda ke bata azumi ta dalilin fitowar maziyi ko ta saduwa ta yadda za ta wajabta kaffarah.

3. Yawan kallon mata don jin sha’awa.

4. Tunani a wurin sha’anin saduwa.

5. Shafa mace da hannu ko rungumarta.

Uzurin Da Yake Halatta Mutum Ya Ajiye Azumi:

1. Ya wajaba ga mai al’ada da mai jinin haihuwa su ajiye azumi.

2. Wanda ke so ya tsamo wani daga halaka da suransu.

3. Matafiyi an halasta masa yin kasru kuma an sunnanta masa ajiye azumi.

4. Marar lafiya wanda ke tsoron cutuwa.

5. Mazaunin gida wanda yayi tafiya da rana, abunda yafi shine yayi azumi don fita daga cikin sabani.

6. Mace mai ciki da mai shayarwa, wadanda suka ji tsoron cutarwa a karankansu ko a kan dan su, koda sun ajiye azumi don tsoron ‘ya’yan su, waliyan su za su ciyar da miskini a ko wane yini bayan haka za su ranka azumi (amma a wurin wasu malaman babu rama azumin, ciyarwa kawai za su yi).

Abubuwan Da Ke Bata Azumi:

1. Riddah (wato fita daga addinin musulunci).

2. Mutuwa.

3. Niyyar karya azumi.

4. Kokwanto game da azumi.

5. Kirkiro amai da gangan.

6. Yin allura mai sa koshi.

7. Fitowar jinin al’ada ko na haihuwa.

8. Hadiye kaki idan ya kawo baki.

9. Kaho: mai yi da wanda aka yi ma (amma a wani zancen, yin kaho baya karya azumi).

10. Fitar maniyyi ta dalilin kallo mai yawa.

11. Fitar maniyi ko maziyi ta sumbanta ko shafa ko istimna’i ko runguma ba tare da saduwa ba.

12. Duk abun da ya isa zuwa makoshi ko makogwaro ko kwakwalwa na wani abu mai ruwa ko waninsa.

Jan Hankali Da Fadakarwa:

Wanda ya sadu da matarshi a cikin watan Ramadan ta gaba ko ta baya, to ramako da kaffarah sun wajaba a kanshi, idan da gangan ya aikata. In kuma ya manta ne, to azumin shi bai baci ba, kuma babu ramako balle kaffarah a kansa. Idan aka tilasta wa mace saduwa da rana cikin watan Ramadan ko ta jahilci hukuncin haka, ko ta manta, to azumin ta yana nan, in kuma an tilasta mata ne to ramako ya wajaba a kan ta kawai, in kuma da gangan ta aikata to kaffarah da ramako sun wajaba a kanta.

Kaffarah: Ita ce ‘yanta baiwa, idan kuma babu sai ayi azumi na tsawon wata biyu a jere, in kuma ba ya yiwuwa sai a ciyar da miskinai sittin, in kuma ba ya da iko to an dauke masa.

Idan mutum ya sadu da matarsa ta dubura, ramako ya wajaba a kansa da kuma tuba zuwa ga Allah.

An sunnanta ramakon azumin Ramadan cikin gaggawa kuma ayi shi a jere, in kuma ya jinkirta har wani Ramadan ba tare da wani uzuri ba, to ramako da ciyarwa sun wajaba a gare shi a kowanne yini.

Duk wanda ya mutu kuma yana da bashin azumin alwashi ko alwashin Hajji, to waliyan sa su ranka mishi.

– Abubuwan da aka so, ko aka karhanta ko aka haramta na azumi:

1. Abubuwan da aka so na azumi: An so yin azumin wadannan ranaku kamar haka:

– Ranar Arafah ga wanda ba mahajjaci ba. Ita ce ranar tara ga watan Zul-Hajji.

– Azumin tara da goma, ko goma da sha-daya na watan Muharram.

– Azumin kwanaki shida na watan shawwal (wato Sittu Sawwal).

– Rabin farko na watan Sha’aban.

– Goman farko na watan Zul-Hajji.

– Watan Muharram.

– Ranakun tsakiya na kowanne wata sune: sha-uku da sha-hudu da sha-biyar.

– Ranakun litinin da alhamis.

– Azumin kwana daya da hutun kwana daya.

– Azumi ga wanda ba ya da karfin yin aure.

2. Azumin da aka karhanta (wato aka ki):

– Azumin ranar Arafah ga mai aikin Hajji.

– Kebe azumin ranar juma’a kawai. (wato ba tare da alhamis ko asabar ba).

– Yin azumi Karshen Sha’aban.

Ya kamata mu sani, yin azumin a wadannan ranaku an hana ne hani na karhanci.

Amma wadanda aka hana hani na haramci, sune kamar haka:

1. Azumin Dore: shine hada azumin kwana biyu ba tare da shan ruwa ba.

2. Yin azumi ranar kokwanto (ranar shakka).

3. Yin azumin shekara ba tare da hutawa ba.

4. Yin azumin mace na nafilah ba tare da izinin mijinta ba, alhali yana gida.

Azumin Da Aka Haramta:

1. Yin azumi ranar bukukuwan Sallah karama ko Sallah babba.

2. Yin azumin ranakun shanya nama, ayyamut-tashrik (ranakun yanyane, ranakun 11, 12, 13 na Zul-Hajji), ga wanda ba mai tamattu’i da bai sami fidiya ba.

3. Ranakun al’ada da jinin haihuwa ga mata.

4. Azumin mara lafiya, rashin lafiya mai tsanani wadda yake ji wa kansa tsoron halaka.

Yadda Ya Kamata Mu Fuskanci Azumin Ramadan A Lokacin Jarabawar Annobar Cutar Korona:

Ya ‘yan uwa, mu sani, Allah cikin ikonsa da hukuncinsa ya kaddara mana wannan jarabawa da ibtila’i na cutar annobar Korona, don haka ya zama wajibi mu dauke shi a matsayin kaddarar Allah, kuma muna fatan Allah ya bamu ladan da yake baiwa masu hakuri yayin da ya jarabcesu.

Sannan ya kamata mu fahimci cewa, rufe wuraren tafsiri da dakatar da Sallar tarawihi ba yana nufin rufe karanta Al-Qur’ani da Sallah da ambaton Allah ba. Muna sane cewa, Allah yana tabbatarwa da bawansa da ladar wani aikin alheri da yake aikatawa a lokacin da wata lalura ta bijiro ta hana shi aikatawa. Sannan hakan kuma baya nuna cewa mu shantake, ya zama tilas mu yi kokari mu dage wurin karatun Al-Kur’ani mai girma da tadabburin ayoyinsa, da yawaita ambaton Allah da Sallolin nafila, da yawaita sadakah da addu’a da kaskantar da kai zuwa ga Allah.

Ka sani idan baka yiwa kanka tsarin da ya kamata ba, to Ramadan zai zo ya wuce ba tare da ka aikata alherin komai ba ba. Mala’ika Jibril yayi addu’a cewa: ya Allah duk wanda Ramadan yazo ya wuce bai yi aikin da Allah zai gafarta masa ba ka turbuda hancinsa a wuta, Annabi yace amin.

Ya Allah ka sadar da mu da Ramadan kuma ka bamu daman aikata alheri kuma ka karba daga gare mu kuma ka sanya mu cikin bayin da za ka ‘yantar daga wuta.

‘Yan uwana, wannan shine abun da Allah ya nufe ni da kawo wa game da bayani akan azumi a takaice.

Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawarka a koda yaushe.

Ya Allah ka bamu lafiya da zama lafiya a cikin kasashen mu da garuruwan mu.

Ya Allah ka kare mu da zuri’ar mu daga cututtuka da fitintinun zamani.

Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunubanmu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW).

Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi a dukkanin al’amurran mu, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author