Yadda ‘yan uwan wadanda suka dawo daga Legas ke kyamatar su a Jigawa – Badaru

0

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru ya bayyana cewa ‘yan uwan wadanda suka dawo daga Legas na kyamatar su, sannan suna gudun su saboda tsoron Korona Baros wato COVID-19.

” Muna ganin yadda wasu mutane ke kyamatar’yan uwan su da suka dawo da jihar Legas saboda tsoron cutar Korona Baros, har sai any i musu gwajin cutar an tabbatar basu da iat kafin su yadda su amince su garwaya da su.

Gwamna Badaru ta fadi haka ne a lokacin da gwamnatin jihar sa ke karbar Almajirai sama da 500 da aka maida su garuruwan su daga Kano.

Badaru ya ce za a killace wadannan almajirai na tsawon kwanaki 14 a sansanonin masu bautar kasa dake jihar. bayan haka kuma za aaika da su ga iyayen su da dan abincin da za su ci.

Amma kuma kwamishinan Ilmin jihar Kano da rako Almajiran ya ce sai da aka hyi musu gwaji a Kano kafin a dawo da su Jigawa.

Share.

game da Author