Wahayin da Allah yayi min game da coronavirus

0

Babban limamin cocin RCCG na kasa fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa Allah yayi masa wahayi game da cutar coronavirus.

Adeboye ya ce ya na daga cikin dalilan da ya sa ya umarci mabiyan sa da su yi azumin kwana 50 daga watan Janairu.

Sannan ya ce Allah ya yi masa wahain cewa zai sa duk duniya a tafi hutun dole a wannan shekara da shine ya sa kuka ga kasashe suna garkame iyakokin su, sannan ana tilasta wa mutane zaman gida don dole.


” Na ji wani manzon Allah ya ce min cutar coronavirus zai mutu, nace masa Amin. Sannan naji kuma wani manzon yana ce mini za a ruwan sama na kwana bakwai da zai wanke cutar a duniya, sai nace Amin. Sai dai kuma ba zai tafi ba kwata-kwata a duniya.

Wannan cuta ta coronavirus Allah ne da kansa yake nuna wa duniya cewa shine mai iko akan komai. Yan iya yin yadda yasa a kowani lokaci sannan da tuantar da su da su dawo ga Allah.

” Ina so kusa ni cewa babu wanda wannan cuta zai kama idan ya yarda da Allah ne zai kare shi kuma yana karkashin kiyayewan Allah ne. Abinda zaka yi shine ka kiyaye ka kuma koma ga Allah. yin hakan shine zai samar maka da kariya.

Akarshe Adeboye ya ce lallai wannan cutar za ta zo ta wuce nan ba da dadewa ba.

Share.

game da Author