Hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu Karin mutane uku da suka kamu da cutar coronavirus a Legas.
Wadannan karin mutane 3 da suka bayyana a ranar Lahadi duk Matafiya ne da suka dawo daga kasashen waje a cikin wannan makon.
Hukumar ta ce duk suna killace a wuri daya ana duba su.
Yanzu mutane 25 me suka kamu da cutar a Najeriya.
Idan ba a manta ba ranar Asabar, NCDC ta sanar cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Ma’aikatar ta ce mutum uku daga cikin suna Abuja sannan 7 a jihar Legas. Ma’aikatar ta ce dukan su sun shigo da cutar daga kasashen waje ne a ‘yan kwanakinnan banda guda daya da ya kamu ta hanyar mu’amula da mutane ne.
Yanzu an samu karin yawan wadanda suka kamu a Najeriya zuwa mutane 23 kenan.
Dukkan su na killace a na duba su.
HANYOYIN KIYAYEWA
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.
Discussion about this post