Cutar Coronavirus, Bayan Dagewa Da Addu’a, Sai Mutane Sun Yi Da Gaske Wajen Bin Ka’idojin Kare Kai, daga Mustapha Soron Dinki

0

Duk abinda yaci yaki cinyewa, maganinsa Allah. Wannan itace akida ta mu’uminai, rayuwar duniya tana tsakanin farin ciki da bakin ciki, rai da ajali, wahala da jin dadi. Haka duniya ta fara, kuma a haka karshenta ma zai zo. Babu wani abu sabo kamar yadda tarihi ya nuna.

Duk musulmi da kirista na gari, a duk inda yake a duniya, ba ma na Najeriya ba kawai, yakamata ya koma ga Allah don neman mafita. Sannan bayan haka, dole sai anyi aiki sosai. Bayan anyi addu’a sai a tsaya ayi aiki tukuru. Wannan itace turbar sunnah.

Mu taimakawa kan mu da bin duk Ka’idojin da suka dace, kada mu dauki yin hakan rashin tawakalli. A’a, ba haka rashin tawakalli yake ba. Musulunci wayayyen addini ne daidai da kowane zamani. Don haka kada musulmai su dauki abun da wasa.

Ita annoba idan tazo, musulunci yace, mutanen da suke cikin yankin da abun ya shafa kada su fita, su kuma wadanda abun bai shafa ba kada su shigo. Wannan kadan daga cikin hikimar musulunci kenan. Kuma shima hakan rigakafi ne sosai. Komai lokaci ne, watarana saidai mu bawa ‘yan baya labari insha Allah.

Rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke, hakan kuma bai bawa dan Adam dama yaqi kula ko kare lafiyarsa ba. Imani ne mutum ya yadda Allah ne zai kareshi kuma sannan imani ne ka yadda da rikon sababi.

Babu dalilin da zai sa kace baka yadda akwai cutar ba, kamar yadda wasu daga cikin mutane masu rauni suke cewa. Duk sanda annoba tazo, magana akan dalilin zuwanta ko rashin yadda da kasancewarta bai taso. Abin da ya dace shine addu’a da bin matakin kauce mata.

Kowa ya fara yin rigakafi tunda daga gidansa, a daure abi Ka’idojin da likitoci suka bayar, duk da akwai Ka’idoji masu alaka da tattalin arziki. Kuma gashi mu muna rayuwa a kasashe wadanda sai a hankali saboda irin salon mulkin da ake yi.

Insha Allah, ba zamu yi gidadanci ba, idan ta kama mu dinga yawo da takunkumi a fuska, da safar hannu da duk abinda ya dace zamu yi don mu riki sababi. Ubangiji Allah ya tsaremu ya kawo karshen wannan annobar.

Allah ya karemu da ikonsa da Iyawarsa. Amin.

Share.

game da Author