Marigayiya Hajiya Aisha Usman: Duk Mai Rai Sai Ya Dandani Mutuwa, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mabuwayi, tsarkakakken sarki. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta, Annabin karshe, Muhammad (SAW), da alayensa da sahabban da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!

Yau laraba, 18/03/2020 na samu labarin rasuwar maman mu, Hajiya Aisha Usman, mahaifiyar Hajiya Maryam Usman, shugabar tawagar mata masu da’awah (wato Women in Da’awah) ta kasa, bayan gajeruwar rashin lafiya. Anyi jana’izarta a babban Masallacin kasa da ke Abuja, bayan sallar azahar. Ina rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya jikan ta, ya gafarta kura-kuren ta da zunubanta, yayi mata sakamako da Aljannah Firdausi, ya kara albarka a cikin zuri’ar da ta bari, amin. Kuma babu abun da zan fada illa kwatankwacin irin abin da Annabi (SAW) ya fada, wato:

“إِنَّ لِلَّهِ مَا أَخَذَ ، وَلَهُ مَا أَعْطَى ، وَكُلٌّ عِنْدَهُ بِأَجَلٍ مُسَمًّى ، فَلْتَصْبِرْ وَلْتَحْتَسِبْ.”

Kuma in kara da cewa:

“عَظَّم الله أجرك ، وأحسن عزاءك، وغفر لميتك، وألهمك صبراً، وأجزل لنا ولك بالصبر أجرا.”
Da kuma:

اللهم اغفر لهاوارحمها، وجعل الجنة مثواها. اللهم اجعل قبرها حفرة من حفرالجنة، اللهم لاتجعل قبرها حفرة من حفرالنار، امين.

‘Yan uwa masu girma, sanadiyyar wannan rashi da muka yi, zan dan yi takaitaccen bayani game da mutuwa da sallar jana’izah a takaice, domin fadakar da ‘yan uwa Musulmi, da kuma nufin Allah ya kai ladar kabarin maman mu, Hajiya Aisha Usman, amin.

Ya ku jama’ah, mu sani, lallai Dan Adam, babu makawa duk yadda yayi rayuwa mai tsawo sai ya mutu. Duk mai rai mamaci ne, kowa sai ya dandani mutuwa ko a nan kusa ko a nesa. Don haka kamata yayi a kowane lokaci mu kasance cikin shirin haduwa da Allah, domin babu wanda ya san lokacin da mutuwa za ta riske shi. Saboda haka mai hankali shine yake tanadin mutuwa a kowane lokaci ta fuskar yin ayyuka nagari tare da kyautata dabi’u da mu’amala. Sannan kuma mu sani, gatan mamaci uku ne da zarar ya mutu, biyu daga ciki za su rako shi bakin kabari, guda daya ne zai zauna tare da shi. Idan mutum ya mutu jama’arsa da dukiyarsa ko matsayinsa za su rako shi bakin kabarinsa, wannan jama’ah da dukiyar za su koma su juya, su bar shi, bayan an gama binne shi. Aikin da ya rika yi kadai zai bi shi har kabarinsa.

Da zarar mutum ya rasu, za’a dauke shi daga gidan aiki (wato nan duniya) zuwa gidan sakamako (wato lahira), yana daga cikin hakkin musulmi akan musulmi ya gaishe shi idan bai da lafiya, kuma ya shaidi jana’izar sa idan ya mutu.

An sunnanta gaida mara lafiya da kuma tunatar da shi yin tuba da yin wasiyyah.

An sunnanta a fuskantar da wanda mutuwa ta halarto mashi ga alkibla, sai a sanya shi mara lafiyan a gefen daman sa da fuskar sa, hakanan idan ba zai cutu ba, in ba haka ba sai a juya shi ya dubi sama kafarsa na fuskantar alkibla, sai a daga kansa sama kadan don ya fuskanci alkiblah, sannan a lakana masa ‘Kalmar shahada’, sai a zuba masa ruwa a makogwaronsa ko wani abin sha, kuma a karanta masa Suratul Yasin (koda yake wasu malamai suna ganin karanta Yasin din bai inganta ba).

Idan mutum musulmi ya rasu, an sunnanta rufe masa ido, da hada masa gemunsa da hada masa kafafunsa da hannuwansa, a kuma dauke shi daga kasa, a cire masa tufafin sa a kuma rufe masa al’aurarsa, a dora shi akan gadon wanka yana kwance gefen dama, kuma yana mai fuskantar alkiblah, idan hakan ya sawwaka, idan ba haka ba kuwa sai a juya kafarsa suna masu fuskantar alkiblah.

Sannan mutanen da ya kamata su wanke mamaci sune wadanda shi mamacin yayi wasiyya da su, sannan babansa, sannan kakansa, sannan na kusa da shi. Ita ma mace wadanda za su wanke ta sune wadanda tayi wasiyyah da su, sannan mahaifiyarta, sannan kakarta, sannan na kusa da ita. Haka kuma kowane miji zai iya wanke matar sa, ita ma mata za ta iya wanke mijinta wadanda suke musulmi.

An yi sharadi mai wanka ya kasance mai hankali, mai wayo masani game da hukunce hukuncen wankan.

An haramta wa musulmi ya binne kafiri, ko ya wanke shi, sai dai yana iya tura masa kasa idan babu wanda zai yi hakan.

Idan za’a yi wa mamaci wanka, sai an rufe masa al’aura, sannan a daga kansa zuwa kwatankwacin yadda zai zauna. Sai a matsa cikinsa kadan-kadan sai a zuba ruwa mai yawa, sannan mai yin wankan za ya sa wani kyalle a hannunsa sai yayi masa tsarki, sannan yayi masa alwala, sannan yayi niyyar wanke shi, sai ya wanke shi da ruwa da magarya ko sabulu, zai ya fara daga kansa da gemunsa, sannan gefensa na dama, sai kuma gefen sa na hagu, sannan ya wanke shi sau biyu zuwa uku kwatankwacin yadda yayi na farko, in bai tsarkaka ba sai ya ta wankewa har sai ya tsarkaka, sai ya sanya wankan karshe ya zama ruwa da kafur ko turare, in kuma ya kasance gashin bakinsa ko farce/kunban sa suna da tsawo sai a cire su, sannan a goge shi da tufafi ko tawul. Ita kuma mace ana yi mata kamu uku na gashin kanta sai a sake su zuwa baya.

An sunnanta ayi wa namiji lifafa (likkafani) farare guda uku, sannan a shinfida su akan juna a sanya masu turare, sai kuma a sanya gaurayayyen turare a tsakanin lifafa, sannan a sanya mamaci a cikin su. Sai a sanya auduga a wasu ramukan jikinsa (kamar dubura) sai a sa masa kyalle daga sama, kamar gajeren wando don ya rufe masa al’aurarsa, sai a sa masa turare a sauran jikinsa. Sannan a sauko da gefen likafanin dake sama a daga bangaren hagu a mayar gefen dama, sannan a sauko da gefen likafanin dama akan hagu, sannan shi ma na biyun haka za’a yi shi, hakanan ma na ukun haka za’a yi shi, sai a sanya abun da ya saura a gefen kan sa, sai a daure a gicciya sai a kabari za’a kwance.

Za’a iya yiwa karamin yaro lifafah (likkafani) daya, kuma ya halatta a yi masa ukun.

Ita kuwa mace ana daura mata zani, sannan a sanya mata riga, sai kuma a daura mata kallabi (dankwali) da kuma riga, bayan an nade ta a lifafa biyu sai a sanya mata riga ayi mata kallabi kuma da dankwali, sannan kuma a nade ta da lifafa biyu. Amma yarinya karama za’a sa mata riga da lifafa biyu.

Ya halatta a wanke mamaci mace ko na miji sau daya, wanda zai game jikinsa gaba daya, haka lifafa daya wadda za ta rufe dukkanin jikin sa.

Idan mace tayi bari, idan ya cika watanni hudu sannan ya rasu to za ayi masa wanka da sallah, kuma a sa masa suna.

Abin da yake Sunnah a sallar jana’iza shine, liman zai tsaya a daidai kirjin namiji, ita kuma mace a tsakiyarta, sai yayi kabbara hudu, yana mai daga hannunsa a kowace kabbara.

Kabbara ta farko zai yi Ta’awwuzi da Basmalah, sai ya karanta fatiha a sirrance, kuma ba zai yi addu’ar bude sallah ba.

Sai yayi kabbara ta biyu, ya karanta Salati ga Anbabi (Salatil Ibrahimiyyah), wato yace:

“اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى ءَالِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى ءَالِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ. وَبَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى ءَالِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى ءَالِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّك حَمِيدُ مَجِيدٌ.”

Ma’ana: “Ya Allah Ubangiji! Ka yi dadin tsira ga Annabi Muhammad da iyalan Annabi Muhammad, kamar yadda ka yi dadin tsira ga Annabi Ibrahima da kuma iyalan Annabi Ibrahima, lalle kai wanda za’a godewa ne kuma mai girma. Kuma ka yi albarka ga Annabi Muhammad da kuma iyalan Annabi Muhammad, kamar yadda ka yi ga Annabi Ibrahima da kuma iyalan Annabi Ibrahima, lalle kai wanda za’a godewa ne.”

Sai yayi kabbara ta uku, sai kuma yayi addu’a ga mamaci yana mai cewa:

“اَللَّهُمَّ اغْفِرْ لِحَيِّنَا وَمَيِّتِنَا، وَشَاهِدِنَا وَغَائِبِنَا، وَصَغِيرِنَا وَكَبِيرِنَا، وَذَكَرِنَا وَأُنْثَانَا، إِنَّكَ تَعْلَمُ مُتَقَلَّبَنَا وَمَثْوَانَا، وَأَنْتَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ. اَللَّهُمَّ مَنْ أَحْيَيْتَهُ مِنَّا فَأَحْيِهِ عَلَى اَلإِسْلاَمِ وَالسُّنَّةِ، وَمَنْ تَوَفَّيْتَهُ مِنَّا فَتَوَفَّهُ عَلَيْهِمَا، اَللَّهُمَّ اَغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ وَعَافِهِ وَاعْفُ عَنْهُ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ وَأسِعْ مَدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِمَاءٍ وَثَلْجٍ وَبَرَدٍ، وَنَقِّهِ مِنَ اَلذُّنُوبِ وَالْخَطَايَا كَمَا يُنَقَّى اَلثَّوْبُ اَلأَبْيَضُ مِنَ اَلدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَارًا خَيْرًا مِنْ دَارِهِ وَزَوْجًا خَيْرًا مِنْ زَوْجِهِ وَأَدْخِلْهُ اَلْجَنَّةَ وَأَعِذْهُ مِنْ عَذَابِ اَلْقَبَرِ، وَعَذَابِ اَلنَّارِ، وَافْسَحْ لَهُ فِي قَبْرِهِ وَنَوِّرْ لَهُ فِيهِ.”

Ma’ana: “Ya Allah ka gafarta wa rayayyun mu, da kuma wadanda suka rasu daga cikin mu, da wadanda suke nan, da wadanda ba sa nan, da manyan mu, da mazan mu da matan mu, lalle kai kasan makomar mu da matabbatar mu, kuma kai mai iko ne akan komai. Ya Allah Ubangiji! Duk wanda ka rayar da shi daga cikin mu to ka rayar da shi akan Musulunci da Sunnah, kuma duk wanda zaka dauki rayuwar shi daga cikin mu to ka dauke ta akan su (wato Musulunci da Sunnah). Ya Allah ka gafarta mashi, ka rahamshe shi, ka yaye masa, ka yafe masa, ka girmama masaukinsa, ka yalwata mashi mashigarsa, ka wanke shi da ruwan kankara da raba, ka tsarkake shi daga zunubai da kurakuransa kamar yadda ake tsarkake farin tufafi daga datti, ka canza masa gida wanda ya fi na shi alheri, da mata wacce ta fi matarsa alheri, ya Allah ka ba shi Aljannah, kuma ka tsare shi daga azabar kabari da kuma azabar wuta, ka kyautata mashi a kabarinsa, kuma ka haskaka mashi a cikin kabarin.”

Idan kuma karamin yaro ne sai yace bayan ya fadi: “Duk wanda zaka dauki rayuwar sa to ka dauke shi a Musulunci da Sunnah”, sai yace:

“اَللَّهُمَّ اَجْعَلْهُ ذخْرًا لِوَالِدَيْهِ، وَفَرَطًا وَشَفِيعًا ومجابا. اَللَّهُمَّ ثَقِّلْ بِهِ مَوَازِينَهُمَا، وَأَعْظِمْ بِهِ أُجُورَهُمَا وَأَلْحِقْهُ بِصَالِحِ سَلَفِ اَلْمُؤْمِنِينَ، وَاجْعَلْهُ فِي كَفَالَةِ إِبْرَاهِيمَ، وَقِهِ بِرَحْمَتِكَ عَذَابَ اَلْجَحِيمِ.”

Ma’ana: “Ya Allah ka sa shi ya zama ajiya da lada da ceto karbabbe ga mahaifansa, ya Allah ka nauyaya mizaninsu kuma ka girmama ladarsu da shi ka hada su da salihai magabata muminai, kuma ka sanya shi cikin rainon Annabi Ibrahim, Ya Allah ka tsiratar da shi daga azabar wuta da rahmarka.”

Sannan sai yayi kabbara ta hudu, sai yayi shiru kadan sannan yayi sallama daya a daman sa.

Ya ku ‘yan uwa na masu daraja, mu sani, duk wanda ya sallaci sallar jana’zah to yana da kwatankwacin lada girman “Kirat” (misalin girman dutsen uhud), in kuma ya bita makabarta har aka binne ta to yana da irin haka biyu.

Sannan an sunnanta cewa mutane hudu su dauki mamaci, kuma an sunnanta daukar mutum guda a makara ta gefen hannun makarar hudu (wato gaba mutum biyu baya biyu kenan), haka kuma a gaggauta yin jana’izah, masu rakiya da kafa su shige gaba, masu abin hawa su biyo baya. Wannan shine Sunnah.

Sannan mu sani, yana wajaba a zurfafa kabari, idan aka kai kasa sai a fafe inda za’a sa mamaci, ana kiran wannan “Lahad”, kuma shine mafi falala akan “Shakku” sai mai sa mamacin a cikin kabarin yace:

“Bismillahi wa ala millati rasulullahi.”

Wato:

“Da sunan Allah, kuma akan addinin Ma’aikin Allah.”

Sai a sa mamacin a lahad ta gafen daman sa yana fuskantar alkiblah, sannan a sa masa hoge (bulo) sosai, sannan a binne shi, a kuma tada kasar gwargwadon kamu daya, sannan kuma a yayyafa masa ruwa.

An haramta yin gini a kan kabari, da kewaye shi da bulo, da yin siminti a kan sa, da taka shi da yin sallah a inda yake, da mayar da wurin masallaci, da neman albarka a kabari, da shafawa don neman waraka, da sanya fitila, da sanya huranni da kuma yin dawafi.

Kuma an sunnanta cewa a aikawa wadanda aka yiwa rasuwa abinci, a aika masu da shi, an hana su yin girkin abinci domin su rabawa mutane. Saboda haka wallahi abincin da ake dafawa daga gidan da aka yi wa rasuwa, ana fitowa da shi kofar gida, ana rabawa masu zaman makoki haramun ne, don haka muji tsoron Allah mu daina yin wannan!

Sannan an sunnanta cewa duk wanda ya ziyarci makabarta ya fadi wannan addu’a:

“اَلسَّلاَمُ عَلَيْكُمْ دَارَ قَوْمٍ مُؤْمِنِينَ، وَإِنَّا إِنْ شَاءَ اَللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، يَرْحَمُ اَللهُ اَلْمُسْتَقْدِمِينَ مِنْكُمْ وَالْمُسْتَأْخِرِينَ، نَسْأَلُ اَللهَ لَنَا وَلَكُمُ اَلْعَافِيَةَ، اَللَّهُمَّ لاَ تُحَرِّمْنَا أَجْرَهُمْ، وَلاَ تَفْتِنَّا بَعْدَهُمْ، وَاغْفِرْ لَنَا وَلَهُمْ.”

Ma’ana: “Amincin Allah ya tabbata a gare ku ma’abotan wannan gida wadanda suke muminai, kuma lallai mu in Allah yaso masu riskarku ne, Allah ya jikan wadanda suka gabata daga cikin ku, da kuma wadanda suka saura, muna roka muna Allah ya yafe muna mu da ku. Ya Allah Ubangiji! Kada ka haramta muna ladan su, kuma kada ka fitine mu bayansu, kuma ka gafarta muna mu da su.”

Kuma an sunnanta yin ta’aziya ga wanda aka yi wa rasuwa kafin a binne mamaci ko bayan binnewar, kuma wannan har tsawon kwanaki uku da dararen su, sai dai ga wanda ba yanan lokacin rasuwar. Don haka ban ga dalilin da zai sa iyalin mamaci su wuce kwana uku suna zama a gidan domin amsar gaisuwar ta’aziyyah ba. Wannan baya da asali a cikin addini, don haka bidi’ah ce. Kuma maimakon suna yi don samar wa mamaci rahama, to sai ya zama sun daukar wa kan su laifi da zunubi!

Kuma an sunnanta cewa ga duk wanda jarabta da musiba suka same shi, na rasa wani nasa ko wani abu mai kama da haka, sai yace:

“إِنَّا لِلَّهِ وَإِناَّ إِلَيْهِ رَاجِعُونَ، اَللَّهُمَّ أَجِرْنِي فِي مُصِيبَتِي وَأَخْلُفْ لِي خَيْرًا مِنْهَا.”

Ma’ana: “Lallai mu na Allah ne, kuma lallai mu gare shi za mu koma. Ya Allah Ubangiji! Ka sakanka mani a masifar nan ta wa, kuma ka mayar man da mafi alherin ta.”

Kuma an halatta yin hawaye ga mamaci, kuma an haramta yaga riga, da bugun kumatu da daga murya, da kururuwa don bakin ciki da takaici da sauran su.

Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tubanmu, ka azurtamu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka.

Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, ga gafartawa dukkanin magabatanmu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW).

Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, a dukkanin al’amurran mu, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author