Buhari ya umarci a rage farashin litan man fetur

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci gidajen man kasa da su rage farashin man fetur.

Ko daya ke sanarwar bai fadi ko nawa bane za a siyar da lita daya na man fetur, shugaba Buhari ya ce ma’aikatar PPPRA zata fadi sabon farashin mai din.

Ministan Albarkatun man Fetur na kasa ne ya bayyana haka a takarda da aka fitar daga ofishin sa ranar Laraba.

Sylva ya ce hakan ya biyo bayan rugujewar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Share.

game da Author