Gwamnatin jihar Kaduna Karkashin gwamna Nasir El-Rufai ta tsara wasu matakai guda bakwai domin rage kashe-kashen kudaden gwamnati a dalilin durkushewar tattalin arzikin duniya da aka fada yanzu.
El-Rufai ya ce dole yanzu fa a rika sara ana duban bakin gatari domin kaf duniya an fada ciki matsalar tattalin arziki a dalilin annobar cornavirus.
Ya ce a Kaduna za adan tsaigata wuta kadan sannan za a dakatar da wasu abubuwan da bai zama dole a yi su ba yanzu domin a tara kudin da za a iya biyan mutane albashi da samun saukin rayuwa.
Ya ce hatta sabbin ma’aikata da za a dauka, za a dakata tukunna zuwa lokacin da abubuwa suka yi daidai kafin a basu takardun samun aiki.
Ga matakan ga gwamnatin Kaduna ta dauka
1 – Gwamnati za ta maida hankali wajen yin manyan ayyukan da ya fi dacewa ne a yi maza-maza tukunna.
2 – Za a rake kashe kudaden ayyukan yau da kullum da kashi 50%, sannan za a hana ma’aikatan gwamnati fita zuwa kasashen waje.
3 – Gwamnati zata kirkiro katin cire kudi na bai daya domin ma’aikatun da ake biya kai tsaye daga sausun gwamnati. Za ayi haka ne domin a rage yin almundahana da kudaden gwamnati da barnatasu.
4 – Za a sake duba yadda ake biyan albashin ma’aikata, za abi shi daki-daki, dalla-dalla domin toshe duk wata kafa da ake barnata kudin gwamnati.
5 – Duk wanda za a dauka yanzu aiki a jihar Kaduna zai dakata tukunna zuwa a samu saukin wannan matsala kafin su fara aiki.
6 – Za a kara matsa kaimi wajen ganin mutane suna biyan harajin kasa da na zama dan jiha.
7 – Suma kananan hukumomi za a sanar musu da kwadaitarda su da su yi irin haka domin a samu daidaituwa.